Ɗangote ya rage farashin fetur zuwa N699

Spread the love

Masana’antar Man Fetur ta Dangote ta sake rage farashin fetur a matakin gangar haya, inda ta saukar da shi daga N828 zuwa N699 ga kowace lita.

Bayanan kasuwa na ainihi da Petroleumprice.ng ta wallafa a ranar Juma’a sun nuna cewa masana’antar ta sake yin babban rangwame, inda ta rage farashin da N129 kowace lita — raguwar kimanin kashi 15.58% kenan.

Wani jami’in masana’antar, wanda ya gana da manema labarai a kan sharaɗin a boye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a bainar jama’a, ya kuma tabbatar da wannan sauyi.

Wata majiya da ke cikin masana’antar ta tabbatar da cewa an rage farashin ne da N129 daga tsohon farashin da ya kasance N828 a lita.

By Babaji