NNPC da wasu gidajen mai sun zaftare farashin fetur

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Farashin man fetur ya sake sauka a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, bayan da Kamfanin Kula da Harkokin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) da wasu manyan masu rarraba man fetur suka rage farashin lita a gudajen sayar da man.

Sabbin bayanai sun nuna cewa a gidajen man NNPCL, farashin ya koma N915 a lita — daga N920 da ake sayarwa baya-bayan nan.

Wasu manyan kamfanonin masu zaman kansu irinsu BOVAS da MRS suma sun daidaita farashin nasu, inda wasu gidajen mai ke sayarwa a N910, bayan da a kwanakin baya ake ganin farashin ya kai N945 a wasu wurare.

Sauran gidajen mai irinsu AYM Shafa, NIPCO, Optima, Mobil, Ranoil da Empire suna sayarwa tsakanin N920 zuwa N937, gwargwadon yankin da gidan man ke da kuma yadda ake samun man daga matatun ruwa da kwantenoni.

Wannan raguwar ta biyo bayan sauƙin farashin man da ake sayarwa a manyan matatun man ƙasa. A ranar Laraba, farashin mai ya tsaya kamar haka:

Dangote – N824.50 a lita

Eterna da Aiteo – N823

BOVAS – N822

Sabon sauƙin farashin NNPCL na zuwa ne bayan sauye-sauye biyu da aka yi cikin makonni biyu da suka gabata, inda farashin ya sauka daga N975 zuwa N945, kafin a sake saukar da shi zuwa N915 a yanzu.

A makon da ya gabata, shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa matsalar dogayen layukan neman man fetur ta zama tarihi. Ya yi alƙawarin cewa za a sami wadataccen man fetur a duk faɗin ƙasar, musamman a lokacin bukukuwan aarshen shekara.

Rahotanni daga sassa daban-daban na Abuja sun tabbatar da cewa jama’a na fara jin sauƙi, duk da cewa akwai bambanciyar farashi tsakanin tashoshi — abin da masana ke danganta shi da hanyoyin samar da man, tsadar sufuri da yanayin arzikin yankuna.

By ukarofi