Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da majalissar zartarwa na masarautar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnati Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya ƙaddamar da sabbin ‘yan majalisar zartarwa masu baiwa sarki Katsina shawara a fannin masarauta.

A jawabin sa
gwamnan ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masarautu, inda ya ce sabbin mambobin majalisar zartarwar za su taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa shugabanci, inganta al’amuran gargajiya, da kuma tattara hankulan jama’a wajen bunƙasa masarautar Daura.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin tallafawa tsarin sarauta da al’adun gargajiya, tare da tabbatar da cewa majalisar zartarwar masarautar ta kasance mai wakilci ga jama’a da kuma masu ruwa da tsaki a al’umma.

Da yake jawabi a madadin sarkin, wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida ya yaba ma Gwamnan Katsina a bisa ƙoƙarin da yake a koda yaushe na ganin an inganta masarautu a faɗin jihar gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa sababbin ‘yan majalisar za su bayar da goyan baya wajen inganta mulki tare da tabbatar da yin adalci a koda yaushe.

’Daga cikin y’an majalissar da aka ƙaddamar na sashen hakimai karaga masu naɗa Sarki sun haɗa da; Kauran katsina Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir, Y’an Dakan Kastina Alhaji Sada Muhammad Sada, Galadiman Katsina Mai shari’a Sadik Abdullahi Muhammad mai ritaya, Durbin Katsina Alhaji Babani Isah Mani sai Marusan Katsina Sanata Hadi Siriki.

Rukuni na biyu sun haɗa da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida, Sardaunan Katsina Alhaji Amadu Rufa’i, Marafan Katsina Alhaji Aminu Marafa, Sarkin Dawan Katsina Alhaji Abba Balarabe sai Sarkin Doka Alhaji Hassan Kabir.

Rukuni na uku sune Sheik Malam Muttaka Gambo Limamin Katsina, Imam Kalid Ayuba, Alhaji Bilyaminu Sanda, Alhaji Muhammad Usman Sarkin a matsayin wakilin matasan Katsina.

Haka ma gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da majalisar zartarwa ta masarautar Daura.

By ukarofi