Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Abu kamar wasa, amma sai rikici tsakanin Shugaban rukunin kamfanonin ɗangote, Alhaji Aliko ɗangote, da Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Malam Farouk Ahmed, ya kai ga cin kujerar shugaban na hukumar ta NMDPRA.
Tun da fari dai ɗangote ya yi kira ga hukumomin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da su gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Malam Farouk Ahmed, kan biyan kuɗin karatun ’ya’yansa a ƙasar Switzerland da ya kai kimanin dala miliyan biyar.
Dangote ya yi wannan furuci ne a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Matatar Man Dangote da ke Lekki a Jihar Legas, inda ya bayyana cewa zargin, idan har ba a bincika shi ba, na iya ƙara raunana amincewar jama’a da masu zuba jari ga tsarin tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ce, an kai masa ƙorafe-ƙorafe daga ɓangarori daban-daban game da wani babban jami’in gwamnati da ake zargi da kashe maƙudan kuɗaɗe wajen karatun ‘ya’yansa huɗu a makarantar sakandare ta ƙasashen waje, lamarin da ya ce ya zama wajibi a bayyana gaskiyarsa a fili.
Dangote ya jaddada cewa idan aka duba albashin jami’in gwamnati da irin kuɗin da ake zargin ya kashe, akwai babban giɓi da ke buƙatar amsa.
A cewarsa, a kowace ƙasa mai bin doka, irin wannan hali zai jawo hankalin hukumomin haraji domin tantance yadda aka samu kuɗin.
Ya nuna damuwarsa kan yadda ake haɗa irin wannan zargi da halin ƙuncin rayuwa da yawancin ‘yan Nijeriya ke ciki, inda ya ce a jihohi da dama, musamman yankunan Arewa, iyaye na kasa biyan kuɗin makaranta na Naira dubu ɗari kaɗai, wanda hakan ke hana yara zuwa makaranta.
“Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, har ‘ya’yana ba su je irin waɗannan makarantun ba. ‘Ya’yana sun yi makarantar sakandare ne a Nijeriya, ba su je ƙasashen waje ba,” inji Dangote, yana mai jaddada cewa ba ya neman a cire jami’in daga muƙaminsa, sai dai a yi sahihin bincike domin tabbatar da gaskiya.
Ya ce, ya dace Hukumar Kula da ɗa’a ko wata hukuma da gwamnati ta ga dama ta tilasta wa jami’in bayyana yadda aka samo kuɗin, yana mai cewa idan har aka ƙaryata zargin, shi a shirye yake ya wallafa bayanan kuɗin makarantar da kuma zaukar matakin shari’a domin a tilasta makarantu su bayyana kuɗin da aka biya.
Dangote ya kuma danganta lamarin da matsin lambar da yake fuskanta a ɓangaren man fetur tun bayan ƙaddamar da matatarsa, inda ya zargi wasu ƙarfi-ƙarfi a harkar mai da cin moriyar shigo da fetur daga waje, maimakon ƙarfafa tacewa a cikin gida.
Ya kammala da cewa barin irin wannan zargi babu amsa na iya zama wata babbar illa ga tattalin arziƙin ƙasa da amincewar jama’a, yana mai kira ga gwamnati da ta tabbatar doka ta yi aiki ba tare da nuna bambanci ba.
Dangote ya miƙa ƙorafi ga ICPC kan shugaban NMDPRA:
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya miƙa takardar ƙorafi ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da rashawa mai Zaman Kanta ta Nijeriya (ICPC), yana zargin Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed, da cin hanci da almundahana.
A cikin ƙorafin da aka miƙa wa ICPC a ranar 16 ga Disamba, Dangote ya buƙaci hukumar da ta kama, ta bincika tare da gurfanar da Farouk Ahmed bisa zargin rayuwa sama da ƙarfin albashin da yake samu a matsayinsa na jami’in gwamnati.
Dangote ya yi iƙirarin cewa Shugaban NMDPRA ya kashe fiye da dala miliyan bakwai wajen biyan kuɗin karatun ‘ya’yansa huɗu a makarantu daban-daban na ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, ba tare da hujjar halalcin kuɗin ba.
Takardar ƙorafin ta bayyana cewa Dangote ya lissafa sunayen ‘ya’yan da makarantu da suka yi karatu a cikinsu, tare da adadin kudin da aka biya domin sauƙaƙa bincike da tantance gaskiyar zargin da hukumar yaƙi da cin hanci za ta gudanar.
A cewarsa, kuɗaɗen da aka kashe ba su dace da dukkan abin da Farouk Ahmed zai iya samu a matsayin albashi ko alawus a duk tsawon aikinsa a ɓangaren gwamnati.
Dangote ya kuma zargi Farouk Ahmed da amfani da ofishinsa da ikon NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen jama’a domin biyan buƙatun kansa da na iyalinsa, abin da ya ce ya janyo fushin jama’a da zanga-zanga daga ƙungiyoyi daban-daban a baya-bayan nan.
Ya jaddada cewa dukkan tarihin aikin Farouk Ahmed ya taƙaita ne a ɓangaren gwamnati, inda kuɗin shigar da ya tara a rayuwarsa ba zai kai adadin dala miliyan bakwai da ake zargin ya kashe kan karatun ‘ya’yansa ba.
A cikin kalamansa, Dangote ya ce irin waɗannan ayyuka sun cika sharuɗɗan laifukan cin hanci, almundahana, karya dokar ɗa’a ga jami’an gwamnati da kuma arzikin da aka tara ta hanyar haram, laifukan da ICPC ke da ikon bincike da gurfanarwa a kansu ƙarƙashin sashe na 19 na dokar kafa hukumar.
Ya ƙara da cewa, dokar ta tanadi hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba idan aka samu mutum da laifi.
Dangote ya bayyana kwarin gwiwa cewa ICPC, a ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Musa Adamu Aliyu (SAN), za ta dauki mataki ba tare da nuna son kai ba, musamman ganin cewa batun ya riga ya shiga idon jama’a. Ya ce hakan zai taimaka wajen kare martabar gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da tabbatar da cewa adalci ya yi aiki.
Ya kuma sha alwashin bayar da dukkan hujjoji da shaidu da ke hannunsa domin tabbatar da zargin cin hanci, almundahana da kuma cin zarafin muƙami da ya ke yi wa Farouk Ahmed, idan hukumar ICPC ta fara cikakken bincike.
Yadda Farouk Ahmed ya yi murabus:
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed, ya yi murabus daga muƙaminsa. Murabus ɗin nasa zuwa ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu ya gayyaci Ahmed ne bayan wasu zarge-zarge da suka shafi cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da harkokin man fetur a Nijeriya.
Tun da farko, hamshaƙin attajirin nan Aliko ɗangote ne, ya zargi Farouk da amfani da ofishinsa wajen yin sama da faɗi da wasu maƙudan kuɗaɗe.
ɗangote, ya miƙa ƙorafi ga hukumar ICPC a ranar Talata, inda ya zargi Farouk da cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Bayan sa’o’i kaɗan da shigar da ƙorafin, ICPC ta tabbatar da karɓarsa tare da bayyana aniyarta ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar a shafukan sada zumunta na ICPC, ya ce “Hukumar ta karɓi ƙorafin ɗangote a hukumance a ranar Talata 16 ga watan Disamba, 2025, ta hannun lauyansa.”
A cikin ƙorafin, “ɗangote ya zargi Farouk da kashe sama da dala miliyan bakwai wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu a ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida, ba tare da bayyana sahihiyar hanyar samun kuɗin ba.”
ƙorafin ya ce Farouk ya yi amfani da muƙaminsa a NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin kansa, lamarin da ya janyo asara ga ’yan Nijeriya.
A nasa martanin, shugaban hukumar NMDPRA, Ahmed Farouk, ya ce yana maraba da binciken da hukumar ICPC za ta gudanarwa a kansa.
Ya ce ya yi imanin cewa binciken zai bayar da dama a duba lamarin cikin adalci da natsuwa, tare da fayyace gaskiyar al’amura domin wanke sunansa.
Ahmed Farouk ya ƙara da cewa ba zai yi musayar zarge-zarge a bainar jama’a ba yana mai cewa zai bari binciken hukuma ya yi aikinsa yadda ya kamata.
ɗangote, ya yi zargin cewa wasu hukumomin kula da harkokin mai na ƙoƙarin hana tace man fetur a cikin gida, yayin da suke barin ana ci gaba da shigo da mai daga ƙasashen waje, abin da ya ce yana nakasa tattalin arziƙin Nijeriya.
Hukumar NMDPRA, wadda Farouk Ahmed ke jagoranta kafin murabus ɗinsa, na taka muhimmiyar rawa wajen kula da shigo da man fetur, farashinsa da rarrabawa a ƙasar.
