Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar ƙwadado ta NLC a Nijeriya, ta ce za ta gudanar da zanga-zangar lumana ta gama-gari, a faɗin ƙasar saboda abin da ta kira ƙara taɓarɓarewar lamuran tsaro a ƙasar.
NLC ɗin ta ce ta na son ganin gwamnati ta ƙara ɗaukar matakan tsaro, domin daƙile wannan lamarin na tsaro a ƙasar baki ɗaya.
Kwamred Nasiru Kabiru, shi ne Sakataren tsare-tsare na ƙungiyar ta NLC, ya shaida wa BBC cewa za su yi zanga-zangar ce saboda nuna ɓacin ransu akan yadda ɓangaren tsaro ya taɓarɓare.
Ya ce,” Idan ka je arewacin Nijeriya tun daga jihohi Borno da Yobe da Zamfara da Sokoto da Kebbi, dukka dai yawancin waɗannan wurare na fama matsalar tsaro, haka idan kaje kudancin Nijeriya ma haka lamarin ya ke.
“Mun yi ta kiraye-kiraye akan gwamnatin tarayya ta tashi tsaye a kan wannan matsala ta tsaro tun da ana kashe ɗumbin ma’aikatanmu da ‘yan Nijeriya da ma talakawan ƙasar, to amma shiru kake ji babu wani abu da ya sauya,” inji shi.
Kwamred Nasiru Kabiru, ya ce,” wajibi ne gwamnati ta bawa al’umma tsaro saboda haƙƙi ne da ya rataya akanta.”
Ya ce,” Idan har Nijeriya na da jami’na tsaron da za su je Jamhuriyar Benin don dakatar da juyin mulki, me zai hana su jami’na tsaron su fara magance ta su matsalar data addabi ƙasarsu, domin batun magance matsalar tsaro a Nijeriya ai ya fi batun daƙile juyin mulki a wata ƙasa.”
“A don haka dole ne mu nuna wa gwamnati bacin ranmu kuma wannan shi ne karo na shida da muka fito muke zanga-zanga akan matsalar tsaro, ƙasar da za ace wai ɗan ta’adda na karɓar haraji ai babu gwamnati,” inji shi.
Sakataren tsare-tsare na NLC a Nijeriya, ya ce,” Mu babban abin da muke so gwamnatin Nijeriya ta yi akan wannan matsala ta tsaro shi ne ta ayyana dokar ta-ɓaci akan tsaro, sannan kuma a kawo shi kashen matsalar cikin gaggawa sannan muna so mu gani a ƙasa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.”
To sai dai a cikin daren Talata Shugaban Nijeriyar Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugabannin ƙwadagon a cikin daren a fadarsa inda a ƙarshenta shugaban ƙungiyar NLCn Joe Ajaero ya shaidawa manema labarai cewa za su tattauna da sauran rassan ƙungiyar domin duba ko za yi zanga-zangar ko a’a.
