
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa MOPPAN, ta miƙa saƙonta na jinjina ga masana’antar Kannywood bisa hoɓɓasa da ta yi wajen fitar da muhimman ayyukan da suka ƙara ɗaukaka darajarta a fannin fasahar wasam kwaikwayo.
A wata takarda da Sakataren MOPPAN ma ƙasa, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel ya fitar, ƙungiyar ta ce furodusoshi sun yi ƙoƙari wajen ganin sun samar wa masu kallo na kowane mataki fina-finai masu ilimantarwa, nishaɗantarwa, faɗakarwa da ƙayatarwa, lamarin da ya taimaka wajen dawo da hankulan masu kallo kan ayyukan masana’antar.
A saƙonta na ƙarshen shekarar 2025, ƙungiyar ta bayyana cewa wasu daga cikin finafinan da Kannywood ta fitar a wannan shekarar sun yi sanadiyyar ɗaukaka martabarta acikin masu sha’awar ayyukansu a nan gida Nijeriya, Nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.
A cewarta, finafinan sun haɗa da Kakanda, Manyan Mata, Garwashi, Labari Na da Wata Shida da kuma Mai Martaba wanda tun a 2024 ya shahara a wajen masu kallo.
MOPPAN ta bayyana cewa, baya ga samar wa ƴan Kannywood aikin yi da haɓaka tattalin arziƙin masana’antar, furodusoshin sun kuma ɗaga darajarta a idon duniya.
Akan haka ne Shugaban ƙungiyar, Shehu Hassan Kano ya yaba da kuma miƙa godiyarsu a gare su da takwarorinsu bisa wannan gagarumar hidima da suka yi wa harkar fim musamman na arewacin Nijeriya.
