‘
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wararrun ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara shida masu ci a ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar Hon. Bashar Aliyu Gummi sun fice daga jam’iyyar su ta PDP sun koma Jam’iyyar APC a jihar baki ɗaya.
‘Yan Majalisar sun sanar da matakinsu a ranar Laraba 24 ga Disamba, 2025, yayin da sukayi zama na musamman a Gusau, babban birnin jihar.
A cewarsu, sun koma Jam’iyyar APC ne bayan rashin biyayya da rashin girmama kundin tsarin mulkin ƙasar da majalisar dokokin jihar Zamfara ta yi.
‘Yan Majalisar sun ƙalubalanci cewa rashin kyakkyawan shugabanci a ɓangaren ‘yan majalisar dokoki a jihar ya taimaka wajen wargaza ayyukanta ta hanyar zamowa ‘yan amshin shatan gwamna Dauda Lawal.
‘Yan majalisar da suka gabatar da wasiƙunsu daban-daban a gaban kakakin majalisar, Honorabul Bashar Aliyu Gummi, sun ce bayan an dakatar da su ba bisa ƙa’ida ba tsawon shekaru biyu yanzu, wanda hakan ya sa aka rufe bakin su a matsayin su na ‘yan majalisa da aka zaɓa, hakan ya Sanya suka kafa tasu wararriyar majalisar dokoki kuma suna ƙalubalantar rashin bin ƙa’idojin ɓangaren da gwamnati ta amince da shi da kuma na zartarwa.
Rahoton Blueprint Manhaja ya nuna cewa ‘yan majalisar da suka sauya sheƙa sun haɗa da kakakin majalisar, Hon. Bashar Aliyu Gummi, ɗan majalisar Gummi, Hon. Nasiru Abdullahi Maru, Barr. Bashir Abubakar Masama, Hon. Bashir Bello, Hon. Amiru Ahmad Keta da Hon. Muktar Nasir Ƙaura.
Sun yi iƙirarin cewa ba tare da su ba, ɓangaren majalisar da ke aiki tare da gwamnan yanzu yana ɗaukar shawara da zartar da dokoki ba tare da samar da cikakken adadin ‘yan majalisar da ake buƙata ba, don haka irin waɗannan dokoki ba su da amfani.
Sun yi kira ga majalisar dokoki ta ƙasa da ta binciki lamarinsu kuma ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa an bi doka sosai a majalisar dokokin jihar Zamfara.
Shugaban wararrun yan majalisar dokokin ta Jihar Zamfara Hon. Bashir Aliyu Gummi ya nuna godiyarsa ga shiga jam’iyyar All Progressive Congress APC.
“Ina ganin wannan shawarar da muka ɗauka itace ingantacciya, kuma za ta inganta zaman lafiyar siyasa a ƙasar mu mai albarka don tabbatar da samun nasarar jam’iyyar APC a jihar a zaɓen dake tafe 2027”. Hon. Gummi ya bayyana
