
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da rahotannin ƙarya da ake yaɗawa cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci a cire Mista Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar tare da maye gurbinsa da Mista Hakeem Muri-Okunola.
Ta bayyana rahoton, wanda ya yaɗu a kafafen Soshiyal Mediya a matsayin “ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma tare da ƙoƙarin haifar da rashin gamsuwa da ayyukan wasu jami’ai acikin gwamnati”.
Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce lallai labarin sallamar Gbajabiamila daga muƙamin, ba gaskiya ba ne don haka ya yi kira ga al’ummar ƙasa da su ƙaurace masa.
Ya bayyana cewa, Gbajabiamila har yanzu shi ne Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, sannan shi kuwa Muri-Okunola zai cigaba da kasancewa babban sakataren harkoki na musamman na fadar.
Haka kuma fadar ta kuma zargi rahoton da ƙoƙarin buɗe ƙofar yaɗa labaran bogi, tana mai gargaɗin ruɗarwa irin haka abu ne da ka iya jefa kokwanto acikin al’umma game da lamuran gwamnati da haifar mata da cikas musamman ganin yadda labarin ya shafi na kusa da ita.
Akan haka ne ta yi kira ga jagororin kafafen watsa labarai da masu amfani da Soshiyal Mediya da su riƙa tabbatarwa tare da tantance labari daga sahihan majiyoyi gabanin yaɗawa.
A ƙarshe, Fadar Shugaban Ƙasar ta shawarci ƴan Nijeriya da su mayar da sahihan kafafen labarai da gwamnati ta amince da su a hukumance a matsayin madogara domin samun labarai na daidai game da harkokin gwamnati.

