MOPPAN ta taya Darakta Nasir B. Muhammad murnar shiga sahun alƙalan Bajekolin Finafinai na Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta miƙa saƙonta na taya murna ga ɗaya daga cikin daraktocin masana’antar Kannywood, Nasir B. Muhammad bisa shiga sahun alaƙan taron Bajekolin Finafinai na Kaduna karo na 9, wato 9th Kaduna Film Festival.

A wata takarda da Sakatarenta, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel ya fitar a ranar Laraba, MOPPAN ta bayyana zaɓar daraktan cikin alƙalan a matsayin “ajiye ƙwarya a gurbinta” duba da kasancewar ƙwararre a fannin.

Ta ce, Nasir B. Muhammad mutum ne da ya ke da ƙwarewa a kowane fanni da ya shafi shirya fim, don haka ake fatan samun nasara wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.

MOPPAN ta kuma yi fatan samun sahihin alaƙanci bisa la’akari da kasancewar sa acikin tawagar alaƙan babban taron.

A ƙarshe, Shugaban MOPPAN, Shehu Hassan Kano da ɗaukacin mambobin ƙungiyar na yi masa fatan alheri wajen ganin an kammala taron cikin aminci da nasara.

By Babaji