Harin Borno: Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a Jihar Borno sakamakon harin bom da aka kai wa wani masallaci a Maiduguri, Babban Birnin jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da jikkata wasu.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da haka a wata takarda a ranar Alhamis, inda ya ce tuni aka baza ƙarin tawagogin jami’an tsaro domin farauto tare da kamo waɗanda suke da hannu a faruwar iftila’in na yammacin Laraba yayin da ake tsaka da sallar Magriba.

Tinubu ya yi tir da harin da bayyana alhininsa akan rayukan da aka rasa, tare da jajenta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.

A nasa jawabin, Mai Girma Kashim Shettima ya jaddada cewa harin ba zai ƙarya ƙudurin Nijeriya na yaƙi da ta’addanci ba, ..”irin waɗannan hare-hare ba za su hana gwamnati cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba”, inji Shettima.

Ya ce, gwamnati za ta ƙara haɗin-gwiwa da jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.

Kakakin rundunar ƴan sandan Borno, ASP Nahum Daso ya shaida wa manema labarai cewa mutane biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da guda 35 suka jikkata.

By Babaji