Shugaban ƙasar Amurka, Donald J. Trump, ya bayyana cewa sojojin Amurka sun kai hare-haren sama kan wasu wuraren da ake zargin ‘yan ƙungiyar ISIS ke amfani da su a Arewac maso Yammacin Najeriya. Wannan sanarwa ta fito ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Truth a daren yau.
A cewar Trump, hare-haren sun gudana ne bisa umarninsa a matsayin babban kwamandan rundunar sojin Amurka, inda ya ce an kai “mummunan hari mai ƙarfi” kan ‘yan ta’addar da ya zarga da kai hare-hare da kashe fararen hula, musamman Kiristoci, a yankin.
Shugaban ya ƙara da cewa ya taɓa gargaɗin ƙungiyar cewa idan ba su dakatar da hare-haren ba, Amurka za ta ɗauki mataki mai tsauri.
Ya ce rundunar tsaron Amurka ta aiwatar da hare-haren cikin nasara, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ci gaban ta’addancin addini ba.
Ya kuma yabawa sojojin Amurka bisa aikin da suka yi, tare da yin fatan alheri ga rundunar, yana mai musu fatan yin bikin Kirsimeti lafiya a ƙarshen jawabin nasa.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Najeriya ko hukumomin tsaro da ke tabbatar da faruwar hare-haren a yankin.

