Ana tafka muhawara kan sabuwar dokar haraji

Spread the love


*Atiku, NBA, Jingir sun tofa albarkacin bakinsu
*Kwamitin majalisa ya kusa kammala bincikensa
*Lambar NIN za ta zama TIN daga shekarar 2026 – FIRS
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tun bayan da ɗan majalisar wakilai daga Jihar Sokoto, Hon. Abdulsammad Dasuki, na Jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa, akwai bambance-bambance tsakanin dokokin harajin da Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince da su da kundin da aka wallafa wa jama’a, ake cigaba da yin muhawara tare da kakkausar suka ga dokar harajin da ake sa ran za ta fara aiki a farkon watan sabuwar shekarar 2026 mai kamawa.
Dasuki, wanda ya yi magana ƙarƙashin Dokar Majalisa ta shida a zauren majalisar ranar Larabar makon jiya, ya shaida wa majalisar cewa abin da aka wallafa a kundin bai dace da abin da ’yan majalisa suka tattauna, suka kaɗa ƙuri’a, suka kuma amince da shi ba.
A cewarsa, bayan amincewa da ƙudirin dokokin haraji, ya ɗauki lokaci a cikin kwanaki uku da suka gabata ya yi nazari sosai kan kwafin da Majalisar ta amince da shi da kuma nau’in da aka daidaita wanda majalisun biyu suka amince da shi, sai ya gano bambance-bambancen.
Saboda haka ɗaiɗaikun jama’a da ƙungiyoyi da kuma masu ruwa da tsaki suka ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tare da sukar lamarin, abin da yawa suka kira da ‘cin mutuncin dimukraɗiyya’.
A nata martanin, ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi kira da a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajin da ake shirin fara aiki da ita a ranar 1 ga watan Janairun 2026.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, NBA ta ce lamarin na tayar da “hankali dangane da sahihanci da gaskiya da amincin tsarin dokokin Nijeriya.”
ƙungiyar ta nemi a gudanar da cikakken bincike a bayyane domin fayyace yadda aka samu dokokin tare da jaddada cewa dole ne a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokar har sai an warware batun.
Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya ce “zargin ya sanya ayar tambaya kan tsari da bin doka wajen samar da dokoki.”
Ya ƙara da cewa “Irin wannan rikici na iya haifar da matsalolin tattalin arziki tare da tayar da hankalin ’yan kasuwa da masu zuba jari da haifar da rashin tabbas ga jama’a da hukumomin da dokar ta shafa.
Canja dokokin haraji cin amanar ‘yan ƙasa ne – Atiku
Haka shi ma tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar PDP, kuma a jigo a ADC, Atiku Abubakar ya ce canjin da ake zargi an samu a ƙudurin haraji da takardun da aka sanya wa hannu cin amanar ‘yan ƙasa ne, sannan karan-tsaye ga kundin tsarin mulkin ƙasa.
Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce sauye-sauyen da aka samu sun nuna cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali ne kan tatsar ‘yan ƙasar sama da taimakonsu.
Jigon siyasar hamayyar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da ƙudurin harajin, wanda ake sa ran farawa a watan Janairun domin gudanar da cikkaken bincike.
Ya kuma buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta yi gaggawar gyara sauye sauye da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, sannan a hukunta masu hannu a yi wa kundin tsarin mulki zagon ƙasa, sannan hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan su.
Ka da ku ɗora mana nauyin da ya fi ƙarfinmu, Sheikh Jingir ga Tinubu
Kazalika Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah ta ƙasa, JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi nazari sosai kan taƙaddamar da ke ci gaba da wanzuwa game da dokokin haraji na Nijeriya, yana mai gargaɗi game da manufofin da za su iya ƙara ɗora wa ‘yan ƙasa wani nauyi.
Sheikh Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin wani lacca ga jama’a a bikin rufe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa ta JIBWIS, wadda aka gudanar a Jos, Jihar Filato.
Malamin addinin Musuluncin ya ce tattaunawa a bainar jama’a da rahotannin kafofin watsa labarai da ke zargin an yi amfani da Dokokin Haraji sun kasance ba a fayyace su ba ga ‘yan Nijeriya da yawa, wanda hakan ya haifar da damuwa da ruɗani a tsakanin jama’a.
Da yake jawabi kai tsaye ga Shugaba Tinubu, Sheikh Jingir ya yi kira da a fayyace gaskiya da taka-tsantsan wajen tafiyar da gyare-gyaren haraji.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu, don Allah, wannan batu tsakanin ku da ‘yan jarida, ba mu san labarinsu ba, kuma ba mu san na gwamnati ba. Da fatan za a duba shi da kyau,” inji shi.
Ya yi gargaɗin cewa idan zargin cewa dokokin haraji za su ƙara ta’azzara wahalhalun ‘yan Nijeriya gaskiya ne, ya kamata gwamnati ta sake duba hanyar da take bi.
“Idan gaskiya ne cewa waɗannan haraji za su cutar da mutane, to kada ku shiga cikin wani abu da ƙila ba za ku iya fita daga ciki ba,” malamin ya yi gargaɗin.
Jingir ya jaddada cewa bai kamata ‘yan Nijeriya su fuskanci manufofi da za su ƙara musu wahala ba, yana mai lura da cewa dole ne shugabanci ya kasance akwai tausayi, adalci, da riƙon amana.
“Mu bayin Allah ne. Kada ku ɗora mana nauyin da ba za mu iya ɗauka ba,” ya yi gargaɗin.
Shugaban JIBWIS ya kuma tunatar da Shugaban game da yanayin shugabancin siyasa na ɗan lokaci, yana mai ƙarfafa tawali’u da jin nauyin shugabanci.
“A da, ba kai ne Shugaban ƙasa ba, kuma da yardar Allah, wata rana ba za ka sake zama Shugaban ƙasa ba,” inji shi.
Kwamitin majalisa ya kusa kammala bincike
Kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincike kan zargin yi wa Dokokin Haraji cushe, ya bayyana cewa zai kammala aikinsa kuma ya gabatar da rahoto nan ba da daɗewa ba.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Muktar Aliyu Betara (Borno, APC), ya yi taro na farko a ranar Talata, 23 ga watan Disamba.
A yayin taron, mambobin sun yanke shawarar kammala binciken cikin sauri don kare doka, tabbatar da bin tsarin doka, da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da aikin majalisar.
Betara, ya tabbatar da cewa za su gabatar da sakamakon binciken da shawarwarin kwamitin nan ba da jimawa ba.
An kafa kwamitin mai mutum bakwai ne domin duba dokokin harajin da aka amince da su, ko sun yi daidai da waɗanda aka fitar a hukumance, bisa tsarin kundin tsarin mulki da ƙa’idojin majalisa.
Dokokin harajin sun haɗa da: Dokar Kafa Hukumar Kula da Haraji ta ƙasa (National Revenue Service Establishment Act), Dokar Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji ta Nijeriya (Joint Revenue Board of Nigeria Establishment Act), Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya (Nigeria Taɗ Administration Act), da Dokar Haraji ta Nijeriya (Nigeria Taɗ Act).
Dokokin sun samu amincewar a dukkanin majalisun biyu a watan Maris, sannan Shugaba Bola Tinubu ya sanya musu hannu a watan Yuni, sannan aka fitar da su a hukumance a ranar 26 ga watan Yuni.
Majalisar ta ɗage zamanta zuwa ranar 27 ga watan Janairu, 2026, saboda bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Lambar NIN ce za ta zama TIN daga shekarar 2026 – FIRS
Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya (FIRS) ta ce daga watan Janairun 2026, Lambar Zama ɗan ƙasa (NIN) da Hukumar Rijistar Katin ɗan ƙasa (NIMC) ta bai wa ‘yan Nijeriya zai kasance lambarsu ta biyan haraji wato TIN, kamar yadda gidan talibijin na Channels ya ruwaito.
Alƙaluman NIMC sun nuna cewa zuwa Octoban 2025, ‘yan Nijeriya miliyan 123 da dubu ɗari tara ne ke da lambar NIN.
A cikin wani saƙon wayar da kan al’umma kan sabuwar dokar harajin da hukumar tattara harajin ta wallafa a shafinta na ɗ, ta ce lambobin rijista da hukumar yi wa kamfanoni rijista ta bai wa kamfanoni zai zama lambarsu ta biyan haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar.
FIRS ta ce sabon tsarin samar da lambar biyan harajin zai kawo sauƙi wajen tantance mutane da kamfanoni, ya rage matsalar nanata sunaye, ya rufe duk wata kafa da ake amfani da ita wajen kaucewa biyan haraji, da kuma tabbatar da cewa duk wanda ke samun kuɗin da ya kamata ya biya haraji ya biya kasonsa.
Hukumar ta ce mutanen da ba su da hanyar samun kuɗaɗen shiga kamar ɗalibai ba sa buƙatar lambar biyan harajin.

By ukarofi