Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, nan da shekarar 2026 ƙasar za ta shiga wani sabon zamani na tsaro da wadata, bayan da ta ce shekarar 2025 ta daidaita manyan ɓangarorin tattalin arziki da tsaro.
Ta ce, shekarar 2026 za ta mayar da hankali ne kan mayar da waɗannan nasarori zuwa ci gaba mai ɗorewa da jin daɗin al’umma.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja.
Ya ce, sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa, shekarar 2025 ta kasance lokacin gina tubali, yayin da manufar shekarar 2026 ita ce gina Nijeriya mai tsaro, gasa da wadata.
Ya jaddada cewa wahalhalun da ake fuskanta sakamakon gyare-gyare na wucin gadi ne, amma ribar da za su haifar na dindindin ce.
Ministan ya ce, hangen nesa na Shugaba Tinubu babba ne, tsarinsa a sarari yake, kuma ƙudurinsa ba ya tangal-tangal.
Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2026, wanda aka yi wa laƙabi da “Kasafin Haɗewa, Juriya da Wadata Ga Kowa,” an tsara shi ne domin zurfafa gyare-gyare, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma buɗe ƙofar gasa a tattalin arziki.
Ya kuma ce shugaban ƙasa ya sha alwashin cewa daga 2026, Nijeriya za ta koma tsarin kasafi guda ɗaya da tsarin samun kuɗaɗen shiga guda ɗaya, tare da fara aiwatar da sabbin dokokin gyaran haraji domin ƙarfafa alaƙar gwamnati da jama’a da kuma tabbatar da gaskiya wajen tara kuɗaɗe da kashe su.
Ministan ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasa ya samu ci gaba mai kyau, inda tattalin arzikin cikin gida ya aru da kashi 3.98 a zangon uku na 2025, yayin da hauhawar farashi ta ragu tsawon watanni takwas a jere zuwa kashi 14.45 a watan Nuwamba 2025.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru zuwa kusan dala biliyan 44.56, yayin da Nijeriya ta samu gibin ciniki na Naira tiriliyan 6.69 a zangon uku na 2025.
A ɓangaren tsaro, Idris ya ce gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin tsaro a faɗin ƙasa, inda ta fara ɗaukar ƙarin sojoji da ‘yan sanda tare da tura masu gadin dazuka a ko’ina.
Ya jaddada cewa duk wata ƙungiya da ke satar mutane ko kai hare-hare kan manoma za a ɗauke ta a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci.
A fagen hulɗa da ƙasashen waje, ministan ya ce dangantakar Nijeriya da Amurka ta ƙara ƙarfi, inda aka warware sabanin diflomasiyya da aka samu ta hanyar tattaunawa cikin mutunci.
Ya bayyana cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwar lafiya ta dala biliyan 5.1 na tsawon shekaru biyar, wadda za ta karfafa tsarin lafiya a Nijeriya.
Ya kammala da cewa sabbin jakadun Nijeriya za su kama aiki a ƙasashen da aka tura su a shekarar 2026 bayan majalisar dokoki ta tantance su, lamarin da zai ƙara ɗaga martabar Nijeriya da ƙarfafa hulɗa da ƙasashen duniya.
