NNPC da hukumomi 12 ba su cika ƙa’idojin aiki – ICPC

Spread the love


Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana cewa, Kamfanin Man Fetur na ƙasa wato NNPC, tare da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya guda 12, sun kasa cika ƙa’idojin ɗa’a da gaskiya, bayan da suka samu maki sifili a sabon rahoton tantance gaskiya da nagartar aiki da hukumar ta fitar.
Rahoton, wanda ICPC ta wallafa a ranar Laraba kuma aka samu kwafinsa, ya nuna sakamakon tantancewar da aka yi wa hukumomi 357 na gwamnatin tarayya a shekarar 2025, inda aka auna yadda suke bin ƙa’idojin gaskiya, tsari da yaƙi da cin hanci a cikin ayyukansu na yau da kullum.
A cewar rahoton, NNPC ce ta zo a ƙarshen jadawalin gaba ɗaya, bayan da ta gaza samun ko maki zaya a dukkan muhimman ɓangarori huɗu da ake amfani da su wajen tantance nagartar aiki. Wannan ya sanya kamfanin a sahun gaba na hukumomin da ICPC ta ayyana a matsayin masu haɗarin rashin gaskiya da tsari.
ICPC ta bayyana cewa, tsarin tantancewar, wanda ake kira ‘Ethics and Integrity Compliance Scorecard’, an ƙirƙiro shi ne domin ƙarfafa gaskiya, ɗa’a da ingantaccen tsari a fannin hidimar jama’a. Tsarin yana duba yadda hukumomi ke tafiyar da al’adunsu na shugabanci, harkokin kuɗi, tsarin gudanarwa, da kuma yadda sashen yaƙi da cin hanci da rashawa ke aiki a cikinsu.
A shekarar 2025, an shigar da hukumomi 360 cikin shirin tantancewar, sai dai uku aka ware, lamarin da ya bar hukumomi 357 aka yi wa cikakken bincike.
Yayin gabatar da rahoton, Shugaban ICPC, Dakta Aliyu Musa, ta bakin Daraktan Sashen Nazari da Bita, Olusegun Adigun, ya ce sakamakon ya tona asirin matsaloli masu zurfi da ke damun tsarin gaskiya da shugabanci a yawancin hukumomin gwamnati.
Rahoton ya nuna cewa hukumomi 48 kacal suka nuna bin ƙa’idoji sosai, yayin da 132 suka nuna bin ƙa’idoji a matsakaici. Hukumomi 141 sun nuna ƙarancin bin ƙa’idoji, yayin da 23 aka ayyana su a matsayin marasa bin ƙa’idoji kwata-kwata. Abin da ya ƙara tayar da hankali shi ne cewa babu ko hukuma guda ɗaya da ta kai matsayin cikakken bin ƙa’idoji.
ICPC ta ƙara da cewa, wasu hukumomi 13 ba su ma bayar da haɗin kai ba yayin tantancewar, abin da ya sa aka lissafa su a matsayin hukumomin da ke cikin haɗari. NNPC ce ta jagoranci jerin waɗannan hukumomi, tare da Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Jami’ar Kalaba, wasu kwalejoji, cibiyoyin bincike da manyan hukumomi a sassa daban-daban na ƙasa.
A gefe guda kuma, Hukumar Kula da Haƙar Man Fetur wato NUPRC ce ta fi kowa samun maki mai tsoka, inda ta samu maki sama da 91. Hukumar Inshorar Ajiya ta ƙasa NDIC, AMCON da Bankin Masana’antu su ma sun nuna kyakkyawan aiki. Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA) ta samu matsayi na 278, abin da ke nuna bin ƙa’idoji a matsakaici.
ICPC ta yi gargaɗi cewa hukumomin da ke ci gaba da samun maki kaɗan ko ƙin amsa kiran tantancewa za su fuskanci ƙarin bincike, nazari da kuma ɗaukar matakan ladabtarwa, domin tilasta musu bin dokoki da ƙa’idojin gwamnati.
Hukumar ta ce, wannan mataki na da nufin inganta gaskiya, lissafi, kwarewa da ingancin aiki a harkokin gwamnati.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ICPC ba ta samu martani daga NNPC ko Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba, duk da yunƙurin da aka yi na tuntuɓar shugabannin su.

By ukarofi