’
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahoton tashar talbijin ta Channels kan harin ƙunar baƙin wake da aka kai wani masallaci a Maiduguri ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin Nijeriya, inda ‘yan ƙasa da dama ke zargin gidan talabijin ɗin da yin amfani da salon da zai iya ƙara rura wutar rabuwar kan addinai domin jawo hankali da samun ƙarin likes a shafukansa.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga Disamba, 2025, lokacin da wani da ake zargi ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari Masallacin Juma’a na Al-Adum da ke cikin kasuwar Gomboru a Maiduguri, Jihar Borno, a lokacin sallar magariba. Rahotanni sun nuna cewa mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu 35 suka jikkata.
An garzaya da wasu daga cikin waɗanda harin ya shafa zuwa Asibitin ƙwararru na Maiduguri, yayin da aka kai wasu zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin samun kulawar gaggawa.
Ce-ce-ku-cen ya tashi ne bayan gidan talbijin na Channels ya gyara wani saƙon da ya wallafa tun farko game da harin, inda ya ƙara kalmar “a daren Kirsimeti”. Masu sukar matakin sun ce hakan ba dole ba ne, kuma na iya haddasa mummunan sakamako a ƙasar da tuni ke fama da gurguwar fahimta ta fuskar addini da ƙabila.
Mataimaki na musamman ga tsohon shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, na daga cikin na farko da suka yi tir da matakin, inda ya zargi tashar da yin abin da ya kira “makircin kawo ruɗani”.
Ya ce, “Da farko sun fitar da labarin ba tare da ambaton Kirsimeti ba. Bayan wasu mintuna, da suka ga bai jawo martanin da suke so ba, sai suka koma suka gyara suka ƙara ‘a daren Kirsimeti’. Wannan rashin hankali ne, kuma yana nuna raunin ƙwarewa da ladabi a aikin jarida a ƙasar nan.”
Wasu kuma sun yi ra’ayi iri ɗaya. Al’ameen Yabo, ya rubutu a shafin ɗ, ya kwatanta kafafen watsa labaran Nijeriya da na ƙasashen waje, yana mai cewa ma kafafen yaɗa labarai na yammacin duniya ba su yin amfani da irin wannan salo wajen tayar da hankali ta kanun labarai.
A cewarsa, “Bayan ‘yan ta’adda, kafafen yaɗa labarai na Nijeriya su ne babbar matsalar wannan ƙasa. Suna janyo rarrabuwa, suna yaɗa ƙiyayya ta hanyar rahotannin da ba a nuna ƙwarewa ba.”
Haka zalika, Mataimakin Mai Ba Gwamnan Jihar Legas Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Wale Ajetunmobi, ya soki gyaran kanun, yana mai jaddada cewa waɗanda aka kashe Musulmi ne da ke tsaka da ibada, ba wai shirye-shiryen Kirsimeti suke yi ba.
Ya ce, “Waɗanda wannan fashewar ta shafa — duk Musulmi ne — ba su yi sallah ne domin Kirsimeti ba. Amma Channels ya nuna babbar rashin kwarewa a aikin jarida ta hanyar karkatar da kanun domin ƙarfafa mummunar farfagandar ‘kisan Kiristoci’.”
Masana harkar sadarwa na ganin irin waɗannan kanun labarai masu ɗauke da ruɗani na iya ƙara dagula zaman lafiya da amincewar jama’a ga kafafen yaɗa labarai. Sun jaddada buƙatar gidajen jarida su rungumi ladabi, daidaito da sanin alhaki, musamman a lokacin rahoton bala’o’i masu alaƙa da tsaro da addini.
A ƙarshe, al’umma na kira ga kafafen yaɗa labarai da su daina neman ɗaukar hankali ta kowace hanya, su mayar da hankali kan gaskiya, mutunci da haɗin kan ƙasa—domin kalma ɗaya kacal na iya ƙara rura wuta ko kuma ta taimaka wajen kashe ta.
