
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya bayyana cewa tarin hare-haren da Amurka ta ƙaddamar a Jihar Sakkwato kuskure ne na abin da aka nufa.
Makama ya faɗi hakan ne yayin da yake tsokaci akan harin da sojojin Amurka suka kai a daren Kirsimeti, inda aka ce an kai harin ne kan ƴan ta’adda, abin da ya jefa al’ummar jihar cikin fargaba da tashin hankali.
A wani faifan bidiyo an ga yadda mazauna ƙauyen Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal suka shiga halin firgici bayan ɗaya daga cikin ababen hare-haren ya sauka a yankinsu kana ya zama wuta mai ban tsoro.
A cewarsa, bayanan sirri da aka dogara da su wajen kai harin ba su wadatar ba, lamarin da ke nuna yiwuwar kuskuren gano wurin da aka kai wa hari.
Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa irin wannan lamari na iya janyo asara ga fararen hula tare da ƙara dagula matsalar tsaro a yankin na Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Ƙwararren masanin tsaron ya kuma buƙaci da a gudanar da bincike na musamman domin gano sahihancin abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da suka dace don kauce wa maimaituwar irin kuskuren a nan gaba, kamar yadda ya bayyana ta kafar X.
