Auren Sakataren gwamnati Akume da tsohuwar matar Oonin ife Zaynab ya tada hazo

Spread the love

Auren Sakataren gwamnati Akume da tsohuwar matar Oonin ife Zaynab ya tada hazo

Daga BELLO A. BABAJI aa Abuja

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume ya auri Zaynab Ngohemba, wadda ita ce tsohuwar matar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, lamarin da ke nuna samun ƙaruwa ta musamman ga ɗaya daga cikin manyan jami’an gwamnati.

Rahoto sun bayyana cewa an sanar da al’amarin ne a ranar Juma’a ta hannun ɗaya daga cikin mambobin iyalan Dajoh, Abraham Double-d Dajoh, ta shafin Facebook.

Iyalan Dajoh sun tabbatar da auren tare da tarbar Sarauniya Zaynab a hukumance zuwa gidan iyali da ke Mbakor a Jihar Benue, a wannan watan Disamba.

Sarauniya Zaynab, wadda asalin sunanta Zaynab Otiti Obanor, ta auri Ooni na Ife ne bayan an gudanar da bikin gargajiya a Benin City, Jihar Edo, a watan Maris 2016, sannan aka ci gaba da shagulgula a Ile-Ife, Jihar Osun. Auren nasu ya ja hankalin jama’a matuƙa, sai dai ya ɗauki kusan watanni 17 kafin ya mutuƙar ƙarewa a shekarar 2017.

Rahotanni da dama nuna cewa Sarauniya Zaynab ta taɓa yin aure a lokuta daban-daban, ciki har da aurenta da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, wani ɗan kasuwa daga Dubai, Ooni na Ife, da kuma wani yarima daga ƙasar Qatar.

A halin yanzu, George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, shi ne mijinta na yanzu.

Wannan al’amari ya janyo cece-kuce acikin al’umma musamman duba da matsayin mutanen biyu da kuma fagen siyasar Nijeriya, al’ada da ma cikin jama’ar ƙasa baki ɗaya.

By Babaji