Nijeriya ta yi watsi da kafa Ƙasar Somaliland da Isra’ila ta amince

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Amurka ta fara ayyukan tattara bayanan sirri da na bincike ta sama a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda take sanya ido kan ƴan ta’adda a dajin Sambisa, bayan hare-hare ta sama da ta kai a daren Alhamis akan mayaƙan ISIS a Jihar Sokoto.

Brant Philip, wanda masanin tsaro ne kuma mai bibiyar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya wallafa bayanan bibiyar jiragen sama da ke nuna wani jirgin Amurka yana shawagi a sararin samaniyar Jihar Borno.

Bayanan sun nuna cewa jirgin da aka yi amfani da shi Gulfstream V ne, wani jirgin kasuwanci mai tafiyar dogon zango, wanda akasari ake amfani da shi domin ayyukan tattara bayanan sirri da bincike na soji.

Wannan haɗin-gwiwar aikin Amurka ya zo ne ƴan makonni kaɗan bayan da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, a Washington.

A wani lokaci ne aka fuskanci tashin hankali sakamakon barazanar da tsohon Shugaba Donald Trump ya yi game da yiwuwar ɗaukar matakin soja a Najeriya kan zargin tauye ƴancin addini da kisan Kiristoci.

By Babaji