Tinubu ya jajenta wa Anthony Joshua bisa hatsari, ya yi jimamin waɗanda suka rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya miƙa saƙonsa na jaje ga tauraron duniya a fannin wasan dambe, Anthony Joshua sakamakon hatsarin da ya rutsa da shi a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da raunata ɗan damben.

A wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya bayyana hatsarin a matsayin ‘faruwar mummunan al’amarin yayin farin ciki’.

“Ina mai jajenta maka da iyalanka yayin da kake jure wannan abin tausayin na faruwar wannan iftila’in”, inji Tinubu.

Shugaban ya ƙara da cewa, a matsayinsa na ɗan wasan mai ƙwazo, horo da soyayyar Nijeriya, hakan ya sa ƙasarta ke alfahari da shi.

Ya kuma yi masa fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci a yayin da yake jinyar raunukan da ya samu a hatsarin tare da fatan Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu.

A jiya Litinin ne al’amarin ya faru a Jihar Ogun da misalin ƙarfe 11 na safe a lokacin da motarsu ta gamu da wata tirela maƙare da kaya.

A wata sanarwar da Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) ta fitar, ta alaƙanta faruwar al’amarin da gudu sama da kima da kuren kerewa.

By Babaji