Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bukaci ’yan Nijeriya su shiga shekarar 2026 da sabon kuduri na gaskiya da rashin amincewa da cin hanci da rashawa.
Olukoyede ya yi wannan kira ne a sakon sabuwar shekara da ya gabatar a Abuja a ranar 24 ga Disamba, kamar yadda wata sanarwa daga shugaban sashen yaɗa labarai da hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ta bayyana a ranar Laraba.
Ya ce duk da farin cikin shigowar sabuwar shekara abin maraba ne, ya kamata hakan ya kuma karfafa wa ’yan Nijeriya gwiwar rungumar ɗabi’un masu kyau domin ba da gudummawa ga ci gaban ƙasa.
“Yayin da muke maraba da sabuwar shekara cikin farin ciki da sabbin fata, mu sabunta kudurinmu mu kuma karkata da karfinmu zuwa hanyoyin gaskiya da rashin amincewa da cin hanci da rashawa,” inji shi.
Olukoyede ya bayyana kyakkyawan fata cewa Nijeriya za ta shawo kan kalubalen tattalin arziki, yana mai cewa ajandar Renewed Hope ta shugaba Bola Tinubu an tsara ta ne domin bunƙasar ƙasa.
