‘Yan sanda sun kama direban Anthony Joshua sa’o’i bayan fitowarsa daga asibiti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Direban motar Lexus SUV da ta yi hatsarin da ya rutsa da tsohon zakaran dambe na duniya, Anthony Joshua, ya shiga hannun hukumar ƴan sanda.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi ya tabbatar da haka a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da ya aike w manema labarai.

A daren ranar ne aka sallamo Joshua daga Asibitin Lagoon da ke garin Ikoyi a Jihar Legas bayan likitoci sun gano ya cancanci cigaba da jinya a gida.

Joshua, wanda ɗan asalin Nijeriya ne, na cikin motar tare da abokai biyu a lokacin da suka yi mummunan hatsari a babban titin Lagas zuwa Ogun, iftila’in da ya yi ajalin abokan nasa.

Rundunar ta bayyana cewa sun tafi da direban ne bayan an sallame shi daga asibiti, domin fara binciken abin da ya janyo hatsarin.

Da fari, bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar gudun wuce ƙima da yunƙurin ratse ne suka sa motar ta ƙwace, inda ta yi karo da babbar motar dakon kaya da aka faka a gefen hanya.

Shidai Joshua ya ji rauni a hatsarin, yayin da abokan nasa, Sina Ghami da Latif Ayodele, da ake yi wa lakabi da Latz suka rasu a nan take.

Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) a wata sanarwa, ta ce mutane biyar ne hatsarin ya rutsa da su inda biyu suka rasu, ɗaya ya samu raunuka, sai kuma biyu suka yi nasarar fita daga motar lafiya.

By ukarofi