Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla lauyoyi 28 ne daga cikin 62 waɗanda aka tsayar domin naɗa su a matsayin alƙalan Kotun Tarayya ta Nijeriya suka tsallake gwajin mutunci da Hukumar Kula da Shari’a ta ƙasa (NJC) ta kafa, yayin da wasu 34 suka faɗi gwajin sakamakon koke-koken da aka shigar kansu, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa lauyoyi 62 ne gaba ɗaya suka shiga jarrabawar kwamfuta (CBT) da Kotun Tarayya ta gudanar, kuma aka tura sunayensu zuwa Hukumar Ayyukan Shari’a ta Tarayya (FJSC).
Sai dai bisa sabon tsari da NJC ta amince da shi a ƙarƙashin Babbar Alƙalin ƙasa, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, an aiwatar da gwajin mutunci ta hanyar buga sunayen lauyoyi domin jama’a su bayar da ra’ayoyinsu kan halayya, suna da cancanta.
Bayan wallafa sunayen a ranar 17 ga Satumba, 2025, an samu koke-koke da dama daga jama’a. ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen ya shafi wata lauya mace da aka zarga da karbar cin hanci yayin aiwatar da aikinta. An miƙa batun ga Hukumar Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), wadda ta tabbatar cewa an karɓi kuɗin Naira Miliyan ɗaya a cikin wata shari’a da ta ratsa ofishinta.
Bisa tabbatar da irin waɗannan hujjoji da sauran koke-koken da aka samu, FJSC ta amince da sunaye 28 kacal da suka tsallake gwajin mutunci, tare da watsar da 34 da suka kasa. Daga bisani an tura sunayen 28 zuwa NJC domin mataki na gaba.
Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan takarar da suka tsallake gwajin za su fuskanci kwamitin hira na NJC kafin taron majalisar da aka shirya gudanarwa a watan Janairu, 2026. Daraktar Yaɗa Labarai ta NJC, Malama Kemi Ogedengbe, ta tabbatar da cewa majalisar za ta yi zama tsakanin 13 da 14 ga Janairu, inda za a tantance lamurran da suka shafi naɗin alƙalan Kotun Tarayya.
Ta jaddada cewa NJC ta ɗauki alƙawarin tabbatar da gaskiya da tsantsar mutunci a tsarin naɗin alƙalan ƙasa, tana mai cewa ba za a sassauta ƙa’idoji ba ko da wane ne ke da hannu. A cewarta, cancanta da mutunci ne kawai za su zama ginshiƙan tantancewa a wannan karo.
