Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gargaɗi ‘yan siyasa cewa shiga APC ko nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu ba ya nufin tabbacin samun tikitin wa’adi na biyu kai tsaye.
Wike ya yi wannan gargaɗin ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ƙaramar Hukumar Emohua da ke jihar Ribas, a wani bangare na ziyarce-ziyarcensa na tuntuɓar jama’a a faɗin jihar.
Ministan, ya samu tarbar Shugaban ƙaramar Hukumar Emohua, Chidi Lloyd, tare da sarkin gargajiya Sergeant Awuse da sauran shugabannin jam’iyya.
A cewarsa, dole ne ƙabilar Ikwerre ta ci gaba da kasancewa mai tasiri a siyasar Nijeriya, yana gargaɗi kan sakaci ko barazanar ware su daga tsarin siyasar ƙasar.
Wike ya bayyana cewa muhimmancin siyasa ana samun sa ne ta hanyar tsare-tsare da daidaito, ba wai a zo a canja tsari bayan an riga an yi nasara ba.
Tsohon gwamnan Ribas ya ja kunnen ‘yan siyasa cewa bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu, musamman bayan zaɓen 2023, ba zai ba su tabbacin samun tikitin tazarce ba.
Ya ƙara da cewa, siyasa dole ta kasance bisa yarjejeniya, tare da cika alƙawura, yana mai cewa biyayya ba tare da tsari ko cika alƙawari ba, ba ta da wani alfanu ga jama’a.
Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar Emohua ya tabbatar da cikakken goyon bayan yankin ga Shugaba Tinubu da Wike, yana mai cewa suna kan tafarkin siyasar da suka zaɓa.
Wike ya ce nuan goyon baya ga Tinubu ba shi zai ba ɗan siyasa damar samun tikitin tazarce ba.
Daga Emohua, Wike ya wuce Isiokpo a ƙaramar hukumar Ikwerre, inda ya maimaita irin wannan saƙo.
A nasa jawabin, Samuel Nwanosike, shugaban hukumar kula da tsafta ta jihar Ribas, ya tabbatar da goyon bayan yankin ga Wike, yana musanta yiwuwar jam’iyyar ADC ta samu karɓuwa a yankin.
Masu lura da al’amura na ganin ziyarce-ziyarcen Wike a ƙasar Ikwerre na nuna ƙoƙarinsa na ƙarfafa tushen siyasar sa, yayin da kalamansa ke nuna yiwuwar sauye-sauyen siyasa kafin zaɓe mai zuwa a jihar Ribas.
