NUT ta karrama shugabannin ƙananan hukumomi da na sashen ilimi a Dawakin Kudu

Spread the love

Daga SUULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Kungiyar Malaman Makarantu ta ƙasa (NUT) reshen ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta karrama Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai-Rago, da Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, tare da Shugaban Sashen Ilimi na Dawakin Kudu, Musa Sani Yankatsare, Shugaban NUT na Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, da wasu malamai bisa nuna hazaka, jajircewa da kulawa ga harkar ilimi.

Da yake jawabi a yayin bikin karramawar, Shugaban NUT na Jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya ce ya zama wajibi ga ƙungiyar su karrama waɗannan shugabanni la’akari da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa harkar ilimi a yankunansu da kuma tasirin hakan ga rayuwar al’umma.

Ya bayyana cewa a lokuta da dama da suka ziyarci yankunan, sun tarar da makarantu cikin lalacewa, rashin kayan aiki, har ma da ofishin sashen ilimi na yankin. Amma a cewarsa, a yau an samu gagarumin sauyi sakamakon kulawa da jajircewar waɗannan shugabanni, inda ilimi ya samu gata a Dawakin Kudu da Warawa.

Baffa Garko ya ce karramawar da aka yi a wannan lokaci na da matuƙar muhimmanci domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da ɗaukar matakai na farfaɗo da ilimi, wanda hakan zai inganta rayuwar al’umma da samar da cigaba mai ɗorewa. Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na shirin karrama shugabannin da manyan lambobin yabo a matakin jiha a yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya da za a gudanar a wannan shekara.

Haka kuma, ya yi kira ga shugabanni da su ƙara tallafa wa malamai da sashen ilimi, musamman ta hanyar samar da ababen hawa domin duba makarantu, kuɗaɗen gudanarwa, da kuma tabbatar da daidaiton albashin malaman firamare da na sakandare da sauran ma’aikatan jiha.

A nasa jawabin, a madadin sauran waɗanda aka karrama, Shugaban Karamar Hukumar Warawa, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, ya yabawa Kungiyar Malamai bisa wannan lambar yabo, inda ya bayyana ta a matsayin abin alfahari da zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ninka ƙoƙarinsu domin ganin harkar ilimi ta ci gaba a yankunansu.

Hon. Lamido ya ce burin gwamnatin su karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shi ne inganta harkar ilimi a faɗin jihar, tare da gina al’umma ta gari. Ya ce ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin jiha ga ilimi duk shekara ya sa ake ganin gagarumin cigaba a fannin ilimi a Kano.

Taron ya samu halartar manyan ’yan siyasa daga Kananan Hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, ciki har da Hakimin Karamar Hukumar Dawakin Kudu, Danmakwayon Kano, Alhaji Yusuf Kabiru, wanda Dagacin gari Alhaji Aminu Usman Bala ya wakilta, da sauran al’umma maza da mata. An gudanar da taron a sakatariyar kula da sashen ilimin firamare ta Karamar Hukumar Dawakin Kudu a ranar Talata da ta gabata.

By ukarofi