Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC ya jefa tafiyar Kwankwasiyya, wadda uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yake jagoranta, cikin ruɗani.
Majiyoyi da dama sun ce, babu gudu, babu ja da baya kan hukuncin da gwamnan ya yanke, ko da kuwa hakan zai kawo cikas tsakaninsa da Kwankwaso.
Sanata Kwankwaso shi ne wanda ya kafa tafiyar Kwankwasiyya kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Abba a zaɓen gwamna a 2023.
Sauya sheƙar Abba da ke tafe ta sake tayar da tsoffin taƙaddama a siyasar Kano, da kuma tambayoyi kan makomar tafiyar Kwankwasiyya, tare da sake fasalin lissafin siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.
Wasu masu kusanci da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun ce ya yanke wannan hukunci ne bayan shawarwari da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ’yan majalisar tarayya daga jihar.
Wani babban hadimin gwamnan, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce rikicin cikin gida a NNPP ce kan gaba wajen sanya gwamnan ya ɗauki wannan mataki, domin a cewarsa, rikicin na barazana ga damarsa ta neman wa’adi na biyu.
“Babban dalili shi ne NNPP ta zama ba ta da ƙarfi saboda shari’o’i da yawa da ake yi a kanta,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, ko da gwamnan ya ci gaba da zama a NNPP, ’yan kanzagin Kwankwaso sun riga sun yanke hukunci cewa ba za su ba shi tikitin takara ba, suna shirin bai wa mataimakin gwamna damar tsayawa.
Majiyar ta ce adawar da ake yi wa Gwamna Abba ta samo asali ne daga tsoron cewa ayyukansa da shaharar da yake samu a faɗin jihar na iya disashe tasirin Kwankwaso.
“Ba sa son ya fi Kwankwaso haske. Ayyukansa a bayyane suke, kuma ba sa son ya ci gaba,” inji shi.
Game da dangantakar Abba da uban gidan siyasarsa, hadimin ya ce aikin gama ya riga ya gama, “Kwankwaso ba ya son wannan gwamna ya dawo. Sabon mutum yake so. Idan APC ta ba shi damar sauya gwamna, zai amince.”
Majiyar ta musanta jita-jitar cewa an tsara ranar sauya sheƙar, inda ta ce hakan na iya faruwa a kowane lokaci. “Ba a tsayar da rana ba. Duk ranar da kuka ji, jita-jita ce. Amma dai, zai faru,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko akwai yiwuwar sulhu, sai ta ce, “To Wa zai shiga tsakani? Waɗanda ya kamata su sasanta sun riga sun ɗauki ɓangare. Kowa ya riga ya yanke hukunci.”
Kwankwasiyya ta rabu gida biyu
Rahotanni sun nuna cewa wannan lamarin ya raba tafiyar Kwankwasiyya zuwa ɓangarori biyu.
ɓangaren farko yana goyon bayan Kwankwaso, kuma ya haɗa da mataimakin gwamna, sanata ɗaya tilo na jam’iyyar, kwamishinoni biyu (na kasuwanci da na kimiyya da fasaha), mai ba da shawara na siyasa ga gwamna da kuma shugaban jam’iyyar NNPP na jihar.
A ɗaya ɓangaren kuma akwai Gwamna Abba, da ’yan majalisar wakilai 13, da kwamishinoni 23, shugaban majalisar dokokin jihar, da ’yan majalisa jiha 19 da dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44.
Wannan ɓangare ana ganin Shugaban Majalisa, Shugaban ALGON da daraktan fadar gwamna na al’amuran gudanarwa ne ke jagorantar sa.
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Kano, Rt Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya tabbatar da ganawarsa da Gwamna Abba a ranar Lahadi, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirin sauya sheƙar gwamnan.
Rurum, wanda yanzu ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya a Majalisar Tarayya ne, kuma ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC kwanan nan, ya ce ba su tattauna batun Kwankwaso a cikin wannan ganawa ba.
“A tsawon tattaunawar ba mu yi maganar Kwankwaso ba. Mun yi gamana ne a kan wasu muhimman batutuwa game da sauya shekara Gwamna, amma ba mu yi maganar tafiyar Kwankwaso ba,” inji shi.
Wasu masu ruwa da tsaki sun shaida wa wakilinmu cewa Kwankwaso ya gudanar da tarob sirri da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Litinin a wani ƙoƙarin ƙarshe da nufin dakatar da sauya shekar, yayin da ’yan majalisar da ke goyon bayan Gwamna Abba suka shirya ganawa da gwamnan domin bayyana goyon bayansu.
Wata majiya da Kwankwaso ta ce, “Kwankwaso ya shiga damuwa sosai kuma a farko bai yarda cewa Abba zai yi masa tawaye a fili ba, Daga dukkan tarurrukan da aka yi, ya bayyana cewa sauya shekar ya kammala. Abin da ake fata kawai shi ne gwamnan ya sake tunani.”
Sulen-Garo zai iya zama mataimakin gwamna
Majiyoyi sun ce a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnan na samun goyon bayan manyan jiga-jigan APC a Kano, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen 2023, Murtala Sule-Garo, domin maye gurbin Abdulsalam. Haka kuma, ana shirin miƙa sunan tsohon ɗan takarar gwamna na APC a 2023, Nasiru Gawuna, a matsayin ɗan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a 2027.
Tun bayan hukuncin Kotun ƙoli kan zaɓen gwamnan Kano, gwamnan ya yi ƙoƙari sosai wajen shawo kan Kwankwaso da ya koma APC.
A watan Nuwamban bara, Manhaja ta rawaito rikicin da ke ƙara tsananta a NNPP ta Kano, inda gwamnan ya ƙaurace wa taruka tare da ƙin ɗaga kiran wayar ubangidansa, Rabiu Kwankwaso.
A shekarar 2024, taken siyasa na “Abba Tsaya da ƙafarka” — wato Abba, tsaya da ƙafarka, ko kuma a ma’ana mafi ƙarfi, Abba, rabu da Kwankwaso — ya yi fice a Kano, yayin da kiraye-kiraye daga cikin jam’iyyar da wajen ta ke ƙara ƙarfi na neman gwamnan ya zama mai cin gashin kansa.
Gwamnan, duk da ya sha alwashin biyayya ga Kwankwaso, ya musanta rahotonmu na Nuwamba 2024 tare da nesanta kansa daga ƙungiyar Abba Tsaya da ƙafarka.
Kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa, bai kai ga amsa kiran waya da saƙon tes ɗin da wakilinmu ya aika masa ba, domin jin martaninsa kan lamarin.
Rikicin tun kafin sauya sheƙa
Majiyoyi sun ce rashin jituwa tsakanin Abba da Kwankaso ya fara ne tun kafin Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki.
An ce Kwankwaso ya nuna sha’awar tattaunawa da APC domin samun muƙami a gwamnatin tarayya, amma tattaunawar ta rushe bayan fadar shugaban ƙasa ta lura cewa buƙatunsa sun yi da kuma barazanar ƙarfafa matsayinsa a Arewa wajen neman mulki a 2031.
Bayan rushewar tattaunawar, shugabannin APC suka karkata ga Gwamna Abba ta hanyar ƙungiyar Gwamnonin APC, abin da ya fusata Kwankwaso.
Wata majiya ta ce a dalilin haka ne Kwankwaso “Yana ganin kamar an raina shi saboda tattaunawar ta ci gaba ba tare da shi ba.”
Wannan saɓani ya kuma taka rawa wajen korar Abdulmumin Jibrin Kofa daga NNPP, bayan Kwankwaso ya zarge shi da yin magana da Tinubu kai tsaye a maimakonsa.
Wata majiya ta ce APC ta fi samun sauƙi wajen tattaunawa da Abba. “Abin da gwamnan yake so shi ne tabbacin wa’adin mulki na biyu. Amma Kwankwaso yana son ikon jam’iyya, muƙaman gwamnatin tarayya ƙasa da tasiri a Kano da Arewa maso Yamma. Wannan ya yi yawa,” inji majiyar.
Shugabannin NNPP sun juya baya
Shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashim Suleiman Dungurawa, ya yi watsi da shirin sauya sheƙar, inda ya roƙi mambobi “don Allah da Manzon Allah” kada su bar jam’iyyar.
Dungurawa ya musanta zargin cewa shugabannin jam’iyya suna ƙoƙarin haddasa sabani tsakaninsu da Kwankwaso, sai dai masu sharhi sun ce adawarsa na iya zama saboda tsoron rasa tasiri idan Gwamna Abba ya tafi da majalisar zartarwa.
Sanata ɗaya tilo na NNPP, Rufa’i Sani Hanga, ya yi watsi da batun sauya sheƙar a matsayin ƙirƙira, yana gargaɗin cewa “’yan Kano ba sa goyon bayan masu cin amana.”
Jam’iyyar ta naɗa Shugaban Riƙo a Kano
Jam’iyyar NNPP ta naɗa Honorabul Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin sabon shugabanta na riƙo a Jihar Kano.
Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar ne ya sanar da naɗin Abiya a wani taron gaggawa a ranar Talata.
Kwamitin ya naɗa Abiya ne bayan karɓar rahoton korar tsohon Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kano, Hashimu Suleiman Dungurawa, daga shugabannin mazaɓarsa.
Manhaja ta ruwaito cewa ranar Litinin da dare shugabannin NNPP na mazaɓar wato Gargari da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, sun sanar da korar Hashimu Dungurawa kan zargin haddasa rikici a jam’iyyar da kuma yi mata zagon ƙasa.
Bayan karɓar rahoton daga Shugaban Jam’iyyar na ƙaramar hukumar, majalisar amince da shi.
Uban Iya bayyana cewa an ɗauki matsayar ne tun mako biyu bayan babban zaɓen da ya gabata.
Kwamitin zartarwar ya karɓi rahoton tare da amince s’da shawarwarin da ke ciki, gami da tabbatar da naɗin Abiya a matsayin shugaban riƙo, domin tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
A jawabinsa, Honorabul Abdullahi Zubairu Abiya ya bayar da tabbacin yin adalci ko kowane ɗan jam’iyyar NNPP da kuma cikakken biyayya ga jagoran Jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sharhin masana
Masani kan siyasa a Kano, Kabiru Sa’idu Sufi, ya ce sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya lissafin siyasa a jihar.
“Mulkin gwamna yana da nauyi, amma zai haifar da rashin jin daɗi,” inji shi, yana gargaɗin cewa NNPP za ta raunana kuma Kwankwasiyya ta rabu gida biyu.
An taɓa danganta Gwamna Abba Kabir Yusuf da APC a baya. Tun bayan hukuncin Kotun ƙoli da ya tabbatar da nasararsa, ake cewa ya riƙa ƙarfafa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar mai mulki.
Gugugwar da ta taso a bara da taken “Abba Tsaya da ƙafarka”, ta nuna kira da neman ’yancin kai, duk da cewa gwamnan ya jaddada biyayyarsa ga Kwankwaso a lokacin.
Sufi ya ce, a matsayin Kano na jiha mai mafi yawan al’umma a Nijeriya, tana muhimmanci a siyasar ƙasa, kuma sauya sheƙar Abba na iya ƙarfafa lissafin zaɓen APC kafin 2027, sai dai kuma matakin ya ƙara tsananta rikice-rikicen cikin gida.
Ga NNPP, rasa gwamna ɗaya tilo na iya rage ƙarfin jam’iyyar zuwa dandalin mutum ɗaya. Ga Kwankwasiyya kuma, wannan mataki na gwada ko tafiyar za ta iya dorewa ba tare da mulki ba.
