Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas sun ƙi karbar kyautar Naira 100,000 da aka tura wa kowannensu a matsayin kyautar Kirsimeti bisa umarnin Gwamna Siminalayi Fubara.
A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa ba ta nemi gwamnati ta tura mata wannan kuɗi ba kuma bai samu sahalewar masu yin doka a jihar ba.
’Yan majalisar sun kuma jaddada cewa, dole ne Gwamna Fubara ya kiyaye tsaro na doka da neman amincewar majalisa kafin ya kashe duk wani kuɗi na gwamnati.
Yayin da ma’aikatan gwamnatin jihar ke cikin murna sakamakon samun wannan kyautar N100,000 daga Fubara, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Enemi George, ya bayyana cewa tura wa ‘yan majalisa waɗannan kuɗaɗen ya saɓa wa ƙa’ida.
George ya zargi gwamnan da ci gaba da amfani da asusun harajin jihar ba tare da amincewar majalisa ba tun bayan rantsar da shi a 2023, sannan ya bayyana cewa mambobin majalisar sun fara ɗaukar matakan mayar da kuɗaɗen ga asusun gwamnati.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu Gwamna Fubara bai gabatar da kasafin kuɗin 2026 ga majalisar ba don dubawa da amincewa, sannan kuma bai miƙa sunayen kwamishinonin da majalisar ta nema ba.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnan yake gudanar da harkokin gwamnati da kwamishinoni takwas kacal waɗanda hukuncin Kotun ƙoli bai shafa ba.
Hukuncin kotun ne da ya amince da Martin Amaewhule a matsayin halastaccen shugaban majalisar dokokin jihar Ribas.
Majalisar ta kuma yi gargaɗi ga wasu ma’aikatan gwamnati da ke haɗa baki da Gwamna Fubara wajen karya tsarin mulki da dokokin jihar Ribas.
Enemi George ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa majalisar za ta ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da bin doka da oda da kuma raba madafun iko.
Majalisar ta ɗage zamanta zuwa ranar 26 ga Janairu, 2026, yayin da taƙaddama tsakanin ɓangaren zartarwa da na doka ke ci gaba da ƙaruwa.
