Daga DAUDA USMAN a Legas
Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah ta ƙasa, reshen Jihar Legas, ta gudanar da taron walimar gasar karatun Alƙur’ani Mai Tsarki karo na goma sha shida, domin ƙara zaburar da yara ɗalibai wajen himmatuwa da koyon karatun Alƙur’ani da tarbiyyar Musulunci.
An gudanar da taron ne a ranar Lahadi da ta gabata a harabar Babban Masallacin Juma’a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan Anfo, a cikin birnin Legas, inda dubban al’ummar Musulmi maza da mata suka hallara domin shaida taron.
Gasar ta gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban Kungiyar Izala na Jihar Legas, Sheikh Imam Malam Suleman Ibrahim, wanda shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Wantauzan Anfo.
Taron ya samu halartar manyan malamai na Kungiyar Izala, shugabannin makarantun Islamiyya da ɗalibai daga unguwanni daban-daban na faɗin birnin Legas.
Daga cikin manyan malaman da suka halarci taron akwai shugaban Majalisar Malamai ta ƙungiyar Izala na Jihar Legas, Sheikh Malam Muhammad Abubakar Arugungu, da limamin Masallacin Juma’a na unguwar Mile 12, Sheikh Malam Buhari Yakubu, da shugaban Kungiyar Izala na Mile 12, Sheikh Malam Muhammadu Guri, da Sheikh Malam Ibrahim, babban na’ibin limamin Masallacin Juma’a na Mile 12, da Sheikh Malam Khali, tare da sauran manyan malamai masu tarin ilimi da kwarewa.
Babban bako a taron shi ne Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma, shugaban Kungiyar Arewa Community na Jihar Legas. Hakazalika, Sheikh Malam Isma’ila Umar, shugaban kwamitin gudanar da gasar karatun kuma babban limamin Masallacin Juma’a na unguwar Marinbich Apapa, shi ne ya jagoranci gabatar da taron tun daga buɗe shi har zuwa kammalawa.
A lokacin wa’azozin da aka gabatar, Sheikh Malam Buhari Yakubu da Sheikh Malam Abubakar Muhammad Arugungu sun jaddada muhimmancin sanya yara a makarantun koyon Alƙur’ani, suna mai bayyana cewa hakan shi ne ginshikin tarbiyya, kyawawan ɗabi’u da makomar al’umma mai nagarta.
Gasar karatun ta ɗauki tsawon kwanaki huɗu, inda daliban makarantun Islamiyya daga sassa daban-daban na Legas suka fafata wajen neman manyan matsayi. Bayan tantance sakamako da alƙalai suka yi bisa ƙwarewa da ƙa’ida, an bayyana waɗanda suka fi kowa bajinta.
A ɓangaren maza, Usama Janaidu daga Alaba Okoko a Karamar Hukumar Iba LCDA ya samu matsayi na farko, yayin da a ɓangaren mata, Hauwa’u Isa Tarai daga unguwar Mile 12 ita ma ta lashe matsayi mafi girma a gasar.
Shugabannin Aungiyar Izala sun bayyana farin cikinsu da yadda gasar ta gudana lafiya, tare da jaddada aniyar ci gaba da shirya irin wannan gasa domin gina al’umma bisa tafarkin Alƙur’ani da Sunnah.
.
