
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya taya Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta ƙasa NRS da aka fi sani da FIRS, Dakta Zacch Adedeji murna bisa zagayowar ranar haihuwarsa.
Tinubu ya kuma jinjina wa ƙoƙarinsa na jagorancin hukumar, wadda tun tsawon shekaru 83 da suka gabata aka kafa ta, inda ya gabatar da sababbin shawarwari, bin salon da ake amfani da su a mataki na duniya cikin ayyukan hukumar, inganta tsare-tsarenta da inganta ma’aikatan domin amfanin ƙasa.
A cewar shugaban ƙasar, shugaban na NRS ya cimma nasarar tara buƙatar kasafin ƙasa a zango na uku na 2025 da kuma taimaka wa cimma nasarar bunƙasa harkar tattali ta hukumar.
Adedeji mai shekaru 48, ya kuma taka rawar gani wajen sarrafa hanyoyin karɓar harajin kayayyakin da ake shigowa da su da waɗanda ake fitarwa, wajen tabbatar da gaskiya da adalci inda ya rage adadin kwanakin ake ɗauka na kammala tantance su daga 21 zuwa 7.
Zacch ya yi aiki a matsayin kwamishinan ilimi a Jiharsa ta Oyo, Sakataren Majalisar Ci-gaban Harkokin Sikari, inda ya samar da Cibiyar Sikari ta Ƙasa da kuma Mataimakin na Musamman ga Shugaban FIRS gabanin naɗa shi a matsayin shugaba a Satumbar 2023.
