Yara 469 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aƙalla yara 469 ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2025, a Jihar Kano, yayin da kashi 51.9 cikin 100 na yara ke fama da rahsin na girma yadda ya kamata.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Farfesa Ruƙayya Aliyu Yusuf na Sashen Nazarin Harkokin Watsa Labarai, Jami’ar Bayero Kano (BUK), a lokacin da take gabatar da takarda mai taken: “Understanding the Basics of Behaɓioural Change: Towards Improɓing Malnutrition in Kano State” a wani taron horaswa ga ’yan jarida.

Farfesa Ruƙayya ta ce rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin kyawawan ɗabi’un cin abinci shi ne babban ƙalubale a Kano, duk da cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen da aka fi haskawa a Global Nutrition Indeɗ.

Ta ce bisa rahoton UNICEF na 2025, kashi 40 cikin 100 na yara ƙasa da shekaru biyar a Nijeriya na fama da nakasu na girma, yayin da a Kano kashi 51.9 cikin 100 ke fama da matsalar.

Farfesan ta nuna damuwa kan lamarin, inda ta ce, “Rashin abinci mai gina jiki na da alaƙa da talauci, rashin wadataccen abinci, ɗabi’ar cin abinci marasa kyau da kuma ƙarancin wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya.”

A nata jawabin, Masanin Kimiyyar Amfanin Gona, Amina Ado Yahaya, ta bayyana cewa Kano ce ke da mafi yawan yara ƙasa da shekaru biyar da ke fama da rashin nauyi, da kashi 42.6 cikin 100, lamarin da ya kamata ya sa a ƙarfafa noman kayan lambu a gida domin inganta abinci mai gina jiki.

Ta kuma ce rashin sinadarin ɓitamin A na daga cikin manyan dalilan makanta a yara, tare da ƙara tsananta cututtuka kamar shan inna da gudawa.

By ukarofi