Taimakon raunana ita ce aƙidar Kwankwaso — Dakta Nisa’i Gwadabe

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Tsohon Shugaban Sashen Kula da Tarihi kuma mataimakin darakta a Sashen Cigaban Karatu na Jami’ar Northwest, Dakta Nisa’i Muhammad Gwadabe, ya bayyana cewa taimakon raunana da marasa galihu ita ce ginshiƙin aƙidar Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Dakta Nisa’i, wanda kuma shi ne sakataren tsare-tsare, manufofi da dabarun tafiyar ƙungiyar Kwankwasiyya Scholars, ya bayyana hakan ne yayin taron ƙungiyar na ƙasa karo na farko da aka gudanar a Kano a makon da ya gabata.

Ya ce taron ya ƙaddamar da masana 318 masu digiri na biyu da na uku, har da farfesoshi, tare da dubban ɗalibai da ke kan karatu a halin yanzu, waɗanda suka amfana da tallafin karatu na Kwankwasiyya. Ya ƙara da cewa, adadin waɗanda suka ci gajiyar wannan tsari ya yi matuƙar yawa fiye da yadda ake zato.

A cewarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fara tsarin tura ’ya’yan talakawa ƙasashen waje domin karatu tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999, ba tare da la’akari da asali, dangantaka ko matsayin iyaye ba. Ya ce shi kansa yana daga cikin waɗanda suka ci wannan gajiyar, duk da cewa bai san kowa ba a wancan lokaci.

Dakta Nisa’i ya jaddada cewa aƙidar Kwankwaso ita ce duk wanda ya samu dama ko gata, ya koma ya taimaka wa waɗanda ba su samu ba, tun daga iyali, unguwa har zuwa al’umma gaba ɗaya, domin samar da adalci da daidaito a rayuwa.

A ƙarshe, ya ce wannan aƙida ce da ake ci gaba da aiwatarwa a ƙarƙashin gwamnatin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda al’umma ke ci gaba da cin gajiyar shirye-shiryen tallafi da bunƙasa rayuwa a fannoni daban-daban. Shi ma Dakta Yusuf Ibrahim Sharaɗa, mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin kasuwancin kafar sadarwa, ya tabbatar da cewa shi ma ya amfana da tallafin Kwankwasiyya Scholars.

By ukarofi