Ganduje ya shirya tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan siyasar Kano bayan dawowarsa Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo gida Nijeriya bayan shafe makonni yana hutu a Dubai ta ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Haka kuma ya shirya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasa musamman waɗanda suka shafi ci-gaba a Jihar Kano.

A wata takarda da Shugaban ma’aikatansa Muhammad Garba ya fitar, Ganduje ya ce ya shirya tattaunawa da ɓangarorin daban-daban da nufin ƙarfafa haɗin kai acikin jam’iyya yayin da alƙiblar siyasar jihar ke ɗaukar wani salo.

Sanarwar ta kuma ƙunshi cewa Ganduje zai kuma shiga a dama da shi a shirin rajistar zama mamban jam’iyyar APC ta yanar gizo, wato ‘electronic membership registration’, shirin da ya samar a lokacin da yake shugaban jam’iyya.

A cewar sanarwar, an samar da shirin ne da nufin zamanantar da tsarin zama mamba a APC, inganta shirin cikin gida da tabbatar da adana bayanan jam’iyyar na daidai kuma bisa gaskiya da sauƙin samu a sassan Nijeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake tsaka da raɗe-raɗin Gwamnan jihar, Abba Kabo Yusuf ka iya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.

By Babaji