Borno: ‘Yan ta’addar da suka sace ciyaman sun nemi a biya fansar Dala 300,000

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ciyaman na Ƙaramar Hukumar Biu da ke Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, Hassan Biu Miringa, ya yi magiya daga komar waɗanda suka yi garkuwa da su, inda ya ce masu garkuwar na neman a biya fansar Dala 300,000 domin sako shi da tare da wani mutum guda da aka tsare.

Rahotanni sun bayyana cewa, Miringa, wanda shi ne ciyaman na ƙaramar hukumar a tsakanin shekarun 2020 da 2022, an sace shi ne tare da wasu kansiloli biyu na gundumomin Zarawuyaku da Miringa a watan Disambar 2025.

Al’amarin ya faru ne akan titin Kamuya zuwa Buni-Yadi, wadda hanya ce da ta yankunan jihohin Borno da Yobe.

An ruwaito cewa, mutanen suan tafiya ne a wata motar Hizbah da ta taho daga Potiskum inda ta nufi Biu, wanda a yayin haka ne ‘yan bindiga suka tare su tare da yin awon-gaba da su da wasu fasinjoji.

Wata majiya ta ce ɗaya daga cikin kansilolin da aka yi garkuwa su tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ta Biu ne da ya sauka a baya-bayan nan, inda ya ƙara da cewa an yi ta magiya ga hukumomin tsaro da su gaggauta ceto su.

Saidai a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga yadda tsohon ciyaman ɗin ke magiya kan cewa ‘yan ta’addar sun nemi a biya fansar Dala 300,000.

Ya kuma kirayi jagororin siyasa da masu faɗa-a-ji na jihar da su gaggauta shiga tsakani a madadinsu.

Daga cikin waɗanda ya ambaci sunayensu akwai mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Umar Kadafur; ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Biu, Kwaya da Shani, Hon. Betera Aliyu; jagoransu, Dakta Sule Ali Rimi; yayansu, Hon. Kimba; da kuma Alhaji Musa Dogo Biu.

By Babaji