Siyasar Kano na rawa yayin da Gwamna Abba ke shirin koma wa APC a yau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Litinin ne ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano zai sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki, lamarin da ke nuna samuwar muhimmin sauyi a siyasar jihar tun bayan zaɓen 2023.

Wani mamban kwamitin zartarwar jihar ya tabbatar da haka ga manema labarai a safiyar Litinin, inda ya ce tuni gwamnan ya kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki a jihar ge da shirin sauya sheƙar.

Ya ce: ” Eh, lallai gwamnan zai koma APC a yau Litinin tare da dukkan magoya bayansa”, inji kwamishinan, wanda bai yarda a bayyana sunansa ba.

A cewar majiyoyin jam’iyya, jam’iyyar APC a Kano tuni ta fara murna da kammala shirye-shiryen tarbar gwamnan da magoya bayan nasa.

Da fari an tsara Abba zai koma APC a ranar 5 ga watan nan na Junairu, inda aka ɗage domin faɗaɗa tattaunawa da tabbatar janyo sauran masu ruwa da tsaki musamman mambobin majalisar dokokin jihar cikin tafiyar.

Ana ganin hakan a matsayin babban suayi a jihar musamman ganin yadda ake gwamnan zai shiga APC ne tare da baki ɗaya ciyamomin ƙananan hukumomin jihar da kuma ‘yan NNPP da ke majalisar dokokin jihar.

Tuni tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya dawo daga Dubai a ranar Lahadi domin halartar taron sauya sheƙar tare da sauran jiga-jigan APC na Kano.

By Babaji