Gwamnatin katsina za ta saki ‘yan bindiga 70 da ke tsare a gidan yari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Katsina ta ce wannan mataki ne na ƙoƙarin ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi da rukunonin ‘yan bindigā da ke addabar sassan jihar.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasir Muazu Ɗanmusa ne ya yi bayani game da yarjejeniyar da aka cimma da ƙoƙarin gwamnati na kiyaye hakan, kamar yadda jaridar Manhaja ta ruwaito.

Ya kuma ce za a saki ‘yan bindigār ne domin ƙarfafa yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin garuruwan da abin ya shafa da kuma ’yan ta’addar da suka tuba a ƙananan hukumomi 15 na jihar.

A cewarsa, wannan yarjejeniyar ta riga ta samar da sakamako mai ƙarfi, inda aka samu nasarar sakin kimanin mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su a baya ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Sai dai wannan mataki na yunƙurin sakin ɓarayin dajin ya haifar da zazzafar muhawara a kafafen sadarwar zamani.

A kwanakin baya ne wata kafar sadarwa ta ruwaito cewa ma’aikatan Shari’a a jihar ta rubuta wa babban mai shari’a inda gwamnatin jihar ke buƙatar sakin ‘yan bindiga 70 da ke tsare gidan gyaran hali.

Kamar yadda ma’aikatan shari’a ta bayyana, buƙatar haka na ɗaya daga cikin yarjejeniyar sulhu tsakanin yan bindiga da al’ummar da abin ya shafa a jihar.

By ukarofi