EFCC Ta buɗe sabon ofishinta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar yaƙi da masu yi ma tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta buɗe sabon ofishinta a cikin garin Katsina.

Kafin nan ofishin hukumar dake shiyar Kano ke kula da jihar Katsina.

Haka nada nufin ƙarfafa yaƙi da masu yima tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa da kawo ƙarshen ayyukan rashawa a Katsina.

Babu wani bayani daga hedikwatar hukumar EFCC ta ƙasa dangane da sabon ofishin.

By ukarofi