Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar ta Safana Hon Abdullahi Sani Safana ya yi wannan alkawari a Ƙauyen Kirtawa yayin da yake ƙaddamar da sabon ofishin rundunar tsaron al’umma a ƙauyen Kirtawa da ke cikin ƙaramar hukumar.
Mai Unguwar yankin na Kirtawa da Babban Limamin ƙauyen su ka buƙaci shugaban ƙaramar hukumar da ya gina masu hanya, asibiti tare kuma da gyara masu makaranta domin inganta rayuwar su.
A cikin jawabin shugaban ƙaramar hukumar Hon. Abdullahi Sani Safana ya yi alƙawarin gina masu asibiti da makaranta, inda nan take ya ɗauki alkawarin gina asibiti a ƙauyen cikin wata ɗaya, zai sa kuma a gyara masu makaranta, bugu da ƙari zai kammala masu masallacin Juma’a na garin.
Ita kuma hanya da suka buƙata, shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar ma da al’ummar yankin, hanyar su tana cikin kasafin kuɗi na wannan shekara ta 2026, kuma da damar ta samu za’ayi ta.
Aikin hanyar za ta fara daga Kukar Samu, tazo Kirtawa, ta wuce Muniya, taje wani gari da ake kira Ɗagwarwa, ta ɓulle zuwa Illela.
A kan buɗe sabon ofishin rundunar tsaron al’umma (Community Watch) a ƙauyen,shugaban ƙaramar hukumar yace” sama da shekara ɗaya kenan da ya bada kwangilar gina ofishin,”Amma saboda matsalolin tsaro da aka sha fama dasu a can baya ya hana a gina ofishin,”inji Safana.
“Kasantuwar samun zaman lafiya a halin yanzu yasa aka bada aikin, gashi kuma har an kammala gina ofishin da zan ƙaddamar domin taimakawa aikin samar da tsaro a yankin,”inji shi.
Ya godewa Gwamnan Jihar Malam Dikko Umar Raɗɗa akan damar da yake basu suna gudanar da ayyukan raya ƙasa ga al’ummar su da ke taɓa rayuwar su kai tsaye.
Sannan shugaban ƙaramar hukumar ya godewa al’ummar yankin kan haɗin kai da goyon baya da suke ba shi wajen gudanar da shugabancinsa.
