An ceto yara 25 da aka sace a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da ceto yara guda 25 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Wase daga hannun ‘yan bindigar da suka yi basaja a matsayin ‘yan bijilante.

Rahotanni sun bayyana cewa tun a ranar 21 ga watan Disambar 2025 ne aka sace yaran a hanyar Zak zuwa Sabon Layi da misalin ƙarfe 7 na yamma a lokacin da suke kan hanyar tafiya zuwa wajen bikin Mauldi.

Uku daga cikinsu sun yi nasarar tserewa yayin faruwar al’amarin, kamar yadda rahotanni suka shaida.

Da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a Jos, Sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau ya bayyana ceton a matsayin ɗaya daga cikin nasarori da hukumomin tsaro suka yi a jihar.

Ya ce, an kai yaran wani waje tare da tsare su na tsawon makonni, inda bayan binciken jami’an gwamnati da na tsaro ne aka samu nasarar ceton.

Ya bayyana cewa, tun a ranar Laraba ne aka gano wurin da yaran suke inda aka same su cikin aminci.

Daga nan ne aka garzaya da su, waɗanda suka haɗa da maza 19 da mata shida zuwa wani asibiti domin tabbatar da lafiyarsu.

Sakataren ya ƙara da cewa, gwamnatin ta ce za ta ɗauki nauyin sadar da su da iyalansu, yana mai jinjina wa hukumomin tsaro bisa hoɓɓasa da suka yi wajen samun nasarar.

By Babaji