Ribas: Har yanzu Fubara bai samu takardar tsigewa a hukumance daga Majalisar Dokoki ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas bai samu takardar tsigewa a hukumance ba daga Majalisar Dokokin jihar kwana uku da ‘ya’yanta 27 suka tada batun tsige shi da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu bisa zargin su da saɓa wa ƙa’idojin aiki.

Bincike daga gidan gwamnatin da Fatakwal a daren jiya Litinin ya nuna cewa, babu wani saƙo a hukumance da aka aike wa gwamnan duk da alƙawarin hakan da Kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya yi.

Wani babban jami’in gidan da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin jagororin, wato gwamnan ko mataimakiyar tasa da ya samu sanarwar tsigewa daga majalisar.

Ya bayyana cewa, a ranar Lahadi gwamnan ya dawo daga ƙasar waje, inda kuma nan da nan ya cigaba da hidindimunsa na gwamnati musamman na harkokin ranar karrama ƙoƙarin sojoji.

To saidai, ana ganin akwai alamun rarrabuwar kai a majalisar yayin da wasu ‘ya’yanta biyu da ke biyayya ga Ministan Abuja Nyesom Wike suka nesanta kansu daga yunƙurin tsige gwamnan.

Tuni ‘yan majalisar, wato Sylvanus Nwankwo da Peter Abbey suka kirayi takwarorinsu da su ƙaurace wa shirin tsigewar tare da neman wata mafita ta warware rikicin siyasar, kamar yadda suka bayyana yayin hira da manema labarai a Fatakwal, ranar Litinin.

By Babaji