Madrid ta naɗa sabon koci bayan sallamar Alonso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jim-kaɗan bayan raba gari da Xabi Alonso, ƙungiyar Real Madrid ta naɗa Alvaro Arbeloa a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.

Arbeloa ya taɓa taka leda a Real Madrid a matsayinsa na ɗan wasan baya, inda ya samu manyan nasarori da kulob ɗin.

Ɗan ƙasar Sifaniyar ya buga wasanni 238 wa Real Madrid daga shekarar 2009 zuwa 2016, inda ya lashe kofunan Champions League biyu da Laliga sau ɗaya da sauransu.

Haka kuma da shi ƙasarsa ta lashe Kofin Duniya na 2010 Euro na 2008 da kuma 2012.

Bayan ya daina wasa, Arbeloa ya shiga aikin koyarwa (coaching) a Real Madrid, inda ya fara daga ƙananan rukunoni har ya kai ga zama babban koci.

By Babaji