Zuwa ga masu ganin sun fi kowa

Spread the love

Ya kai mai karatu, ina rubuta maka ne ba da alƙalami na fushi ba, amma da tawada ta nasiha; ba da murya ta tsinuwa ba, amma da numfashin tausayi. Ina rubuta maka ne domin na ga wata cuta mai shiru tana yawo cikin zukatanmu, tana sanya mutum ya ɗauki kansa a matsayin madubi ɗaya tilo, ya ga sauran mutane a karkace. Ita ce cutar girman kai, wadda take sa mutum ya ɗauka cewa shi ne mizani, shi ne ma’auni, shi ne hanyar tsira, sauran kuwa duk sun ɓace.

Allah Maɗaukaki ya riga ya gargaɗe mu game da wannan hali tun fil azal, inda Ya ce: “Kada ka ɗauki kanka tsarkakke; Shi ne Mafi Sanin wanda ya kiyaye.” (Suratul Najm: 32).

Wannan aya kamar madubi ce da Allah Ya ɗaga a gaban zuciyar mutum, domin ya kalli kansa ba ƙarara. Domin duk wanda ya ce “ni na fi kowa”, to ya riga ya faɗi jarrabawar tawali’u.

Ya kai mai ɗaukar kanka gaba da kowa, ka tuna cewa ilimi da fahimta ba mallakin mutum ɗaya ba ne. Allah Ya halicci mutane mabambanta, Ya raba basira, Ya bambanta fahimta, Ya sanya kowa da nasa gwagwarmaya.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya ke da kwayar girman kai a zuciyarsa ba zai shiga Aljanna ba.” Sai wani ya tambaya: “Ya Manzon Allah, kada nutum ya sanya tufafi masu kyau kenan?” Sai ya ce: “Allah Mai Kyau ne, Yana son kyau; girman kai shi ne ƙin gaskiya da raina mutane.”

Wannan Hadisi yana tsaga zuciya kamar wuƙa, domin yana bayyana cewa matsalar ba tufafi ba ce, ba ilimi ba ne, ba muƙami ba ne; matsalar ita ce raina waninka, ka ƙaryata gaskiya idan ba daga gare ka ta fito ba.

A yau, muna rayuwa ne a zamanin da kalma ɗaya take iya raba al’umma gida biyu. Mutum ya faɗi ra’ayi, sai wani ya ce masa kai ɓata-gari ne. Wani ya yi kuskure, sai a gaggauta yi masa hukunci kamar Allah Ya ba mu izini. Alhali kuwa Allah Ya ce: “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku nisanci yawan zato, domin lalle wasu zato zunubi ne.” (Suratul Hujurat: 12).

Idan Allah Ya hana mu zato, wa ya ba mu ikon yanke hukunci kan zukatan mutane?

Ya kai mai ganin hanya ɗaya kacal, ka tuna cewa Annabi (SAWW) shi ne mafi cika, mafi tsarki, mafi kusanci ga Allah, amma duk da haka yana cewa: “Ni ma ina mutum ne, ina kuskure kamar yadda kuke kuskure.” Idan Annabi ya koyar da mu tawali’u, to mu wa ne da za mu ɗaga ƙirji mu ce mu ne mizanin gaskiya?

Wasiƙa ta ba ta zo domin ta zage ka ba, ta zo ne domin ta tashe ka daga barcin ƙaryar cika. Domin girman kai kamar hazo ne; yana sa mutum ya ga kansa babba, amma ya makantar da shi daga ganin gaskiya. Wanda ya ɗauki kansa tsarkakke, ya riga ya rufe ƙofar gyara. Wanda ya ce “ni na fi kowa”, ya riga ya ɗauki kansa a matsayin abin bautawa, ko da bai sani ba.

Allah Ya ce: “Kuma kada ka yi tafiya a doron ƙasa da girman kai; lalle ba za ka tsaga ƙasa ba, kuma ba za ka kai tsayin duwatsu ba.” (Suratul Isra’i: 37).

Wannan aya kamar murya ce daga sama tana cewa: ka sauko, ka tuna asalinkA, ka tuna ƙarshe naka. ƙasa ce za ta rungume ka, ba kursiyin girman kai ba.

Ka kalli tarihi, za ka ga cewa mafi yawancin rikice-rikice, fitinu da rarrabuwar kai sun taso ne daga tunanin “mu ne gaskiya, kowa ɓatacce ne”. Alhali Allah Ya halicci duniya domin jarrabawa, ba domin kowa ya zama alƙali ba. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya ce ɗan uwansa kafiri ne, ɗayan su ya dawo da kalmar.” Wannan gargaɗi ne mai nauyi, yana koyar da mu yin hattara da harshe da zuciya.

Ya kai mai karatu, ka sani cewa tawali’u ba rauni ba ne, hikima ce. Sauraron waninka ba rangwame ba ne, balaga ce. Yarda cewa kai ma kana iya kuskure ba ƙasƙanci ba ne, tsira ce. Domin Allah Yana ɗaukaka mai ƙasƙantar da kansa, Yana ƙasƙantar da mai ɗaukaka kansa.

Ina rufe wannan wasiƙa da addu’a, ba da hukunci ba. Ina roƙon Allah Ya tsarkake zukatanmu daga girman kai, Ya ba mu idon da zai ga alheri a wurin waninmu, Ya ba mu kunne da zai saurari gaskiya ko da daga bakin wanda ba mu so ta fito. Domin a ƙarshe, ba wanda zai tsira da “ni”, sai da “Ya Allah Ka gafarta”.

Idan ka ji wani abu daga cikin wannan wasiƙa ya taɓa zuciyarka, to ka sani rahama ce, ba zargi ba. Domin nasiha kyauta ce daga zuciya zuwa zuciya. Allah Ya sa mu kasance masu tawali’u, masu adalci, masu tausayi. Amin.

Daga Injiniya Mustapha Musa. 08168716583

By ukarofi