Musulunci a Amurka

Spread the love

Alhamdulillahi, Babban Birnin New York ya shiga sabon babi na tarihi a ƙarƙashin shugabancin Musulmi, lamarin da bai yi wa shugaban Amurka Donald Trump da wasu irinsa daɗi ba. Duk da yadda wasu ke kallon wannan lamari da ido na shakku, gaskiya ita ce samun Zohra Muhammad Mamdani a matsayin jagorar birnin New York wata babbar baiwa ce daga Allah ga addinin Musulunci. Wannan al’amari ya kara tabbatar da cewa duk inda makiya ke ƙoƙarin hana hasken addini, sai Allah Ya ƙara bayyana shi.

Allah Ya ba Zohra Muhammad Mamdani nasara a wannan zabe da aka yi a ƙasa irin Amurka, inda ta fafata da ‘yan takara da dama, ciki har da wadanda ba Musulmai ba. Wannan nasara ta zo ne a ƙasar da tarihi ya nuna ta yi yaki da Musulmai a lokuta da dama, kamar hare-haren da aka kai Afghanistan a 2002 da kuma Iraki a 2003. Baya ga haka, a ƙarƙashin mulkin Donald Trump, Amurka ta dauki matakai da dama da suka shafi nuna wariya da tsangwama ga Musulmai, har ma da yunƙurin bayyana cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya, alhali lamarin bai kai haka ba.

Tabbas, a yau duk mai hankali zai yarda cewa Allah na cika hasken addininsa, ko da makiya sun ƙi. Wannan nasara ta Zohra Mamdani hujja ce karara da ke nuna cewa Musulunci ba ya gushewa, sai dai yana kara ƙarfafa.

Da fatan Allah Ya ba wannan baiwar Allah, Zohra Muhammad Mamdani, ikon gudanar da mulki cikin sauƙi, adalci da hikima, domin duniya ta ga tasirin adalcin Musulunci a aikace, kamar yadda ta kudurta tun daga ranar 01/01/2026. Allah Ya taimaketa, Ya ƙarfafeta, Ya kuma tsare dukkan Musulmai a ko’ina suke daga sharri da fitina. Amin.

Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA, Katsina. 0706434519/08080140820

By ukarofi