
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Litinin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta raba gari da mai horar da ‘yan wasanta, Xabi Alonso.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan da ƙungiyar ta sha kaye a hannun Barcelona a wasan ƙarshe na gasar Super Cup.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce sun amince su rabu da Alonso ne ta hanyar fahimtar juna domin a rabu lafiya.
“Za mu cigaba da girmama Xabi Alonso a Real Madrid kuma yana da daraja da wuri na musamman.”
Ta ƙara da cewa, tana godiya da gudunmuwar da ya bayar wajen horas da ‘yan wasan nata gami da masa fatan alheri a gaba.
Alonso ya lashe wasa 24 cikin wasa 34 a cikin wata takwas da ya yi na jagorantar Madrid.
