Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Na san mutane da dama cikin Yan uwanmu, ba za su yarda da ni ba kan zabo shi a matsayin gwarzon Arewa a wannan shekara ta 2025 sakamakon banbancin akida. Ni ma ba mai bin akidar ƙurani zalla ba ne, amma ga dalilai na, na zabensa a matsayin babu gwarzo kamarsa a shekarar da ta gabata.
Bara iwar haka, na tabbata mutane Yan kalilan ne su ka san Yahaya Masussuka, domin ni kaina ban san shi ba. Amma zuwa karshen shekarar 2025, da wahala ka sami wani Dan Arewa mai mu’amala da kafofin sada zumunta wanda zai ce bai ji labarinsa ba. Ya fara shekarar 2025 da mabiya Yan dubunnai a social media, amma a watanni ukun karshen shekarar ta kai kusan a kullum ya na samun akalla mabiya dubu a kowacce Rana, inda ya kammala shekarar da mabiya sama da 200,000 kuma ya zama wanda ya fi kowa gaggawar samun mabiya.
Abin tambaya shine, menene ya jawo masa irin wannan farin jini, musamman ga matasa, duk da cewa a baya ita wannan akida ta ƙurani zalla kamar mujiya ta ke tsakanin Musulmin Arewa? Dalilan su na dama. Na farko dai a yan shekarun nan, malamai da dama sun fara fitowa karara su na sukar wasu hadisai da nuna rashin yarda da ingancinsu. A kurkusa mun ga dambarwar Sheikh Abduljabbar a Kano da Malaman Salafiyya yadda a karshe ya janyo masa zaman kurkuku.
Hatta a cikin Malaman Salafiyya, irin su Ahmad Gumi, sun zo da wasu ra’ayoyi da ake ganin sun sabawa fassarar gama-gari ta wasu hadisai, da ra’ayoyi da su ka ci karo da na jamhuru. Misali kan maganar Riba, kashe wanda ya yi batanci da maganar ta’addanci da sulhu da ya. Ta’adda.
A ɗaya gefen, masu nazari da bincike irin mu, mun dade muna cewa dole sai an saka sikeli a kan hadisai domin tantance su ta hanyar amfani da ma’aunin ƙurani, kimiyya da tarihi. Wadannan abubuwa ya sa matasa da dama sun yi marhabin da fitowar Yahaya Masussuka.
Matasa da su ka yi Boko da zurfi, musamman wadanda su ka nazarci kimiyya, sakamakon yadda mulhidai ke amfani da kimiyya wajen kalubalantar addinai, ya kan sakawa wadanda ba su yi zurfin Ilimin addini ba, su ke samun raunin Imani yadda wasu ma ke karbar akidar Mulhidanci. A nan Kano mun ga yadda Dan Malam Jafar ya shiga wannan akida, haka Dan Dr Bala Muhammad, wato Mubarak Bala, wanda har Kurkuku ya tafi sakamakon batanci ga Musulunci. Akwai Dan wani babban Soja da ya dawo daga Japan ya karbi addininsu (Buddhism ko Shinto). Haka Dan Nasir El Rufai an ce ya zama mulhidi. To ina dalilin da yayan elite, ba na talakawa kadai ba, ke karbar Mulhidanci? Saboda malamai ba sa iya basu amsoshi gamsassu kamar yadda kimiyya ke zuwa musu da bayanai na zahiri. Sannan ba’a iya ba su amsoshi na falsafa da su ka jibanci ubangiji, Lahira, Rai da wasu tambayoyi masu tsauri.
Waɗannan dalilai na kishirwar Ilimi daga matasa da kuma gazawar Malaman gargajiya wajen dora matasa a gwadaben tunani, na daya daga cikin dalilan da su ka jawowa Masussuka farin jinin matasa.
Sannan adawar Malaman Salafiyya, wadanda su ne su ka mamaye social media, inda Sheikh Isa Pantami ke sama da mabiya 1.9, sai Sheikh Daurawa, Sheikh Guruntum, Sheikh Abdulwahab, Sheikh Gumi, Dr Bashir Aliyu, Sheikh Gadon Kaya dss ya janyo engagement na mabiyansu da yawa wajen sukar Masussuka, wanda haka ya kara masa matukar tagomashi yadda ya zama a wannan shekara babu wanda ya ke samun habakar magoya baya cikin gaggawa irinsa.
Yanayin yadda ya ke da’awa, ta hanyar amfani da barkwanci da falsafanci, ya yi matukar tasiri ga masu kallonsa. Irin sunayen barkwanci da ya ke sakawa yawancin Malaman Izala da ke sukar da’awarsa da muzanta shi ta hanyar kiransa Dan kala-kato ko Dan Tatsine, hakika ya sa bidiyoyinsa sun zama tamkar comic clips, wato abubuwan bada dariya, ga wasu mutane. Kasancewarsa ba ya nuna fushinsa, kullum cikin fara’a da Raha ya ke raddi, shi ma ya ba shi tagomashi. Haka nan kasancewa ya na da fikira ta tunani kuma ya na aiki da tunani wajen raddinsa shi ma ya ja masa mabiya.
Salon Malaman Izala na amfani da gwamnati wajen titsiye malamai, wadda ta yi sanadin tura Abduljabbar kurkuku, kuma su ka yi kokarin gwamnatin jihar Katsina ta titsiye Masussuka, shi ma ya ja masa farin jini a wajen wasu.
Tasirin Masussuka, a gani na, ba na yada akidar ƙurani zalla ba ce, domin akasarin masu bin sa, zaka samu ba zasu rungumi akidar kai tsaye ba, amma abubuwa da ya kawo na Dora mutane a gwadaben a yi tunani da kallon ayoyin ƙurani a matsayin hukuncin farko, shine gagarumar gudunmuwa da ya kawo Arewa. Shekaru da dama muna da’awar cewa lallai sai Musulmi sun koma sun dauki abubuwa uku idan su na son samun nasara. Wato bin tarbiyar ƙurani da Allah ke kiran mu, da mu yi “Tafakkuri da tadabburi”, mu bar kowa a kan akidarsa, mu dabbaka ƙurani farko. Wadannan abubuwa su Masussuka ke jaddawa, kuma duk wanda ke kishin Musulunci dole ya ɗabbaka su.
Kuskuren Masussuka shine na cewa a yi watsi da hadisi, kamar yadda wasu yan kala-kato su ka dade su na da’awa a kai, irinsu Dangungun. Amma na ga ya fara karkatowa wajen karbar wasu hadisai da ba su yi karo da ƙurani ba, ko batanci ga Manzo ko kuma assasa ta’addanci. Hakika wannan sassauci na sa a kan hadisai abin a yaba ne, domin ya nuna cewa zai iya karbar gyara, tunda a baya da’awar ita ce ta ƙurani zalla.
Abu na ƙarshe, wanda ya baiwa Masussuka tagomashi a Arewa, shine kokarin hada kai da yan dariku da kuma jawo Kiristoci kusa da kiran a zauna lafiya tare da baiwa kowa yancin yayi addininsa. Duk mai nazari ya san cewa Allah ya umarce mu a ƙurani da mu baiwa kowa yancin addini, mu zauna lafiya da makwabtanmu cikin Amana ko da akwai sabanin akida ko addini. Kuma karara, hakan rayuwar Annabi ta nuna a Madina. Domin ya bada yancin addini da kariyar rayuka da dukiyoyi na abokan Amana.
A taƙaice za mu gane cewa farin jinin Masussuka ya sami asali daga wasu bukatu ne na jama’ar Arewa, wato kashe kishirwar Ilimi daga hujja ta ƙurani ba shaci fadi na malamai ba, yancin fadar ra’ayin addini, Raha a koyar da addini, zama lafiya da sauran tarikoki da Kiristoci. Wato duk abubuwa ne positive wadanda zasu kawo hadin kai da ci gaba. Kuma babbar illar da ta ke kawo adawa tsakanin masu bin ƙurani zalla da sauran akidu ita ce watsi da Hadisi gaba daya, kuma Masussuka ya fara janyewa ta bin wadancan kaidoji na hadisan da ba zai karba ba, wato ka ga ya yarda da wasu hadisai kenan.
Bisa hujjojin sama, Masussuka zai ci gaba da karbuwa tsakanin al’ummar Arewa a shekaru masu zuwa, yadda matasa da dama za su bi ra’ayinsa a abubuwa da dama, koda kuwa sun saba a ainihin aƙida.
A karshe mu gane cewa matasa a Arewa na kishirwar Ilimi, zamani ya zo musu da kimiyya da technology wanda ke biya musu bukata amma addini ba ya basu irin amsoshin da zasu gamsar da su. Shi yasa kada mu yi mamakin yadda hatta Mulhidanci ke kwasar samarin Arewa ballantana akida irin ta Masussuka wadda Alherinta ya bayyana a zahiri. Ya kamata Musulmin Arewa mu farka daga barci mu gane cewa bamu da illar da ta wuce ta rarrabuwar kawuna da yakar juna, yayin da makiya ke barcinsu muna yi musu akinsu.
Na jinjina wa Masussuka a matsayin gwarzona a wannan shekara sakamakon zaburar da Arewa, muna fata Allah ya kawo mana irinsu daga kowacce irin akida ko addini, wadanda zasu farkar da mu daga barcin da mu ke yi, mu yi amfani da kwakwalwar mu wajen tunani da kuma hada kawunanmu don kawo ci gaba da zaman lafiya a wannan yankin namu.
Malam Ali manazarci ne a Kano. Za a iya samun sa a [email protected]
