Jami’ar UNIMAID ta wanke ɗaliban da aka zarga da alaƙa da Boko Haram

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta ƙaryata ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kama wasu daga cikin ɗalibanta akan zargin su da alaƙa da mayaƙan Boko Haram, tana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.

Rijistiran jami’ar, Ahmada Lawan ya bayyana haka a wata takarda da aike wa jaridar NewsPointNigeria sakamakon yawo da wani faifan bidiyo ke yi akan al’amarin, wanda ya tayar da hazo musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce, babu wani ɗalibin jami’ar da bincikensi ya nuna cewa yana da wata alaƙa da ‘yan Boko Haram ko wata ƙungiyar masu tsatstsauran ra’ayi.

Lawan ya ƙara da cewa, jami’ar ba ta taɓa lamuntar kowane yanayi na nuna tsatstsauran ra’ayi, tashin-tashina ko wani aiki da ka iya zama barazana ga tsaron ƙasa.

Kazalika, ya ce UNIMAID tana aiki tuƙuru wajen ganin ta yaƙi dukkan al’amuran da za su taimaka wa yaɗuwar dukkan abin da zai zama fitina ga al’umma da ciyar da zaman lafiya gaba musamman a shiyyar.

A ƙarshe, jami’ar ta roƙi al’umma da su ƙaurace wa labarin da yaɗa shi a matsayin batu mai haɗari, tana mai jaddada aniyarta ta yin fintinkau a fannin ilimantar da al’umma.

By Babaji