Tallafin rage talauci na N50,000 na ƙarfafa tattalin arzikin al’ummar Kano – Gwamna Yusuf

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shirin tallafin rage talauci da ƙarfafa tattalin arziki na N50,000 duk wata da gwamnatinsa ke aiwatarwa an tsara shi ne domin bai wa masu amfana damar taka rawar gani wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar rabon jari ga masu cin gajiyar shirin a ɗakin taro na Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa shirin rage talauci wani ɓangare ne na cika alƙawarin da gwamnatinsa ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ayyana shekarar 2026 a matsayin shekarar ƙarfafa tattalin arzikin maza, mata da matasa a wani ɓangare na yunƙurin daƙile talauci da haɓaka hanyoyin samun abin dogaro.

A cewarsa, tun daga hawansa mulki ake ci gaba da aiwatar da shirin ba tare da yankewa ba, inda dubban mata suka riga suka amfana tare da samun gagarumin sauyi a rayuwarsu.

Yana jaddada tasirin shirin, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa ya samu rahoton wata mata da ta zuba tallafin N50,000 da ta fara samu a cikin sana’a, inda ta bunƙasa jarinta zuwa sama da Naira miliyan 1.2 cikin shekaru biyu.

Kazalika gwamnan ya shawarci sabbin masu amfana da su yi amfani da kuɗaɗen cikin hikima domin tallafa wa iyalansu tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’ummominsu.

Haka kuma, ya yaba wa ko ɓgggghvMajalisar Dokokin Jihar Kano karkashin jagorancin Kakakinta, Hon. Jibril Ismail Falgore, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar, bisa goyon bayan da suka bayar ta fuskar dokoki da kuma sakin kuɗaɗen shirin a kan lokaci.

A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Jibril Ismail Falgore ya ce ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen rage talauci da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun bayyana ƙarara a sassan jihar.

Ya ƙara da cewa har ma masu sukar gwamnatinsa sun amince da irin sauyin alheri da Gwamna Yusuf ya kawo a Jihar Kano.

Tun da fari, yana jawabi a madadin Kungiyar Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON), Mataimakiyar Shugaba kuma Shugabar Karamar Hukumar Danbatta, Alhaji Jamilu Abubakar Dambatta, wanda ya wakilci Shugabar kungiyar, Hajiya Sa’adatu Yushau Soja, ya yaba wa Gwamnan bisa jagoranci mai adalci da kunshewa kowa.

Sannan ya ta yabawa shirye-shiryen da ke bai wa al’umma damar zama masu amfani, da dogaro da kai da samun kwanciyar hankalin kuma tattalin arziki.

By ukarofi