
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Lahadi ne Moroko da ke jagorantar gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025 za ta fafata da takwararta ta Senegal a wasan ƙarshe.
Hakan na zuwa ne bayan da ƙasar ta doke ‘yan Super Eagles na Nijeriya da ci 4 da 2 a bugun fenariti a daren jiya Laraba yayin wasan dab da na ƙarshe.
An ƙare wasan babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu a zangon mintina 90 da na ƙarin rarar lokaci, lamarin da ya kai su ga zangon fenariti.
‘Yan wasan Super Eagles, wato Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi ne suka rasa damar zura ƙwallayensu a raga. Hakan ya ba Moroko damar nasara duk da ita ma ta kasa zura ƙwallo guda.
Da fari Senegal ta su Sadio Mané ta doke Misra ta su Mohammed Salah da ci 1 Mai ban haushi a ɗaya wasan.
