
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwar Nigeriy da ke Jihar Kano kuma Shugabansu, Dakta Bature Abdulazeez Adakawa, ya rasu a ranar Asabar.
Za a gudanar da sallar jana’izarsa ne a yau Lahadi da ƙarfe 10 na safe a gidansa da ke ’Yankaba a Birnin Kano.
Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa kwanaki shida da suka gabata an yi zama da shi a gidansa, inda aka tattauna kan makarantar Ta’adibul Aulad Adakawa.
Haka kuma, a ranar Talata, marigayin ya kai ziyarar ta’aziyyar Malam Mansur Manzo.
Mutuwar attajirin ta girgiza al’umma, musamman ‘yan kasuwa da abokan hulɗa, ganin irin rawar yake takawa wajen ci-gaban kasuwanci da ayyukan alheri acikin al’umma.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, Ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makoma a gare shi.
