Fim ɗin ‘Kitso Da Kwarkwata’: Yadda sunansa ya bi shi tun farkon farawa

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A kwanakin baya kaɗan da suka gabata ne aka kammala ɗaukar wani sabon fim mai suna ‘Kitso da Kwarkwata’, wanda kamfanin shirya fina-finai mai suna Goldin Pin Multimedia ya ɗauki nauyin shiryawa. Mustapha Adam Muhammad shi ne ya zamo jagoran shirin, inda aka yi amfani da jarumai masu yawa – kama daga tsofaffin jarumai da kuma sababbi. 

Fim ne mai dogon zango, wanda da zarar an kammala shi za a nuna shi a manyan gidajen talabijin da kuma manhajar YouTube da sauran manhajojin kallo.

Kamar yadda binciken Blueprint Manhaja ya tabbatar ma na, farkon shirya fim ɗin tun daga rubuta labarin, samar da jarumai, guraren ɗaukar shiri har zuwa ranar farko da aka fara ɗaukar aikin komai ya tafi daidai.

Sai dai a rana ta biyu da fara aikin, sai ɗaya daga cikin jaruman aka gano tana rashin lafiya. Wannan ya jawo dole sai da aka sauya ta da wata bayan ɓata lokaci da kuma asarar kuɗi.

Bayan an sauya jarumar aikin fim ɗin ya fara  tafiya. Sai kuma ɗaya daga cikin jaruman wadda tana cikin masu muhimmanci a fim ɗin ta ce tafiya ta same ta zuwa Abuja. Tafiyar ta ke da wuya kawai sai aka gano ta a cikin wani aikin fim da ake yi a wani gari ba Abuja ɗin da ta ce za ta je ba. Wannan ma ya taɓa aikin fim ɗin sosai ta ɓangaren kashe kuɗin samar da wajen aikin da shirya jarumai da za su yi aikin, domin jarumar ta tafi da cewar za ta dawo a kwana biyu, amma sai da ta haura kwana goma.

Wata matsalar da ta sake jefa fim ɗin ‘Kitso da Kwarkwata’ cikin garari a aikin ita ce rashin zuwa jarumai a kan lokaci, duk lokacin da aka tsara za a fara aikin, sai ya zama ga ma’aikatan sun shirya amma jaruman da suke da muhimmanci a aikin ba su zo ba. Wannan shi ma ya ƙara jefa fim ɗin cikin wani yanayi na kashe kuɗi tare da jan lokaci wajen aikin. Domin shi aikin fim ɗin ‘Kitso da Kwarkwata’ an tsara za a kammala aikin a kwana goma sha shida, amma sai da aka yi kwana ashirin da huɗu ana aikin, ban da zaman jira da aka yi na tsawon wata guda, saboda matsalar da jaruma ta biyu wadda ta yi karyar zuwa Abuja ta bayar, wannan ya sa a jimlace, aikin fim ɗin ya shafe tsawon watanni biyu da kwanaki.

Jagoran shirin Al-Mustapha Muhammad Adam ya ce waɗannan abubuwan da suka faru ya nuna sun yi ‘kitso da kwarkwata a wajen ɗaukar jaruman fim ɗin, in da yake cewa: “Gaskiya wannan abin da ya faru ya taɓa mini zuciya sosai. Saboda mutanen da nake ganin za su taya ni mu samar da wani abu da kowa zai amfana kuma ya kawo mini matsala wanda nake ganin hakan a matsayin cin amana. Kuma hakan ya jawo mini asara, domin bayan canza jarumar farko, ita wannan ta biyun da ta tafi da ƙaryar za ta dawo a kwana biyu, wannan ta sa na fuskanci ƙalubale da yawa a wajen aikin, don har sai da na yi tunanin ko ma ina da ciwon zuciya. Domin sai a ɗan wannan lokacin muka kammala aikin, ko shi ɗin ma sai da wasu dabaru muka samu muka toshe wasu matsalolin.”

A game da gundarin labarin fim ɗin kuwa Al-Mustapha Muhammad Adam ya bayyana mana cewar ” Shi labarin fim ɗin ‘Kitso da Kwarkwata’, labarin cin amana ne wanda ya biyo bayan sakaci da maigida yake yi a game da iyalinsa. Inda wani maigida ya bar matarsa cikin wani yanayi, ita kuma tana buƙatar sa a kusa da ita, amma sai ya fifita kasuwancin sa a kan iyalansa. Haka nan ya tsare ‘yarsa ba ya buƙatar ta kula kowa. To a wannan gaɓar ne aka samu kitso da kwarkwata.”

Ko da muka tambaye shi cewa a yanzu an kammala ɗaukar zangon farko, za a ci gaba ne ko dai ana gudun sake yin kitso da kwarkwata a na gaba?

“To gaskiya ne sunan wannan fim ɗin ya bi shi wato kitso da kwarkwata, tun a farkon fari na zaɓi jarumar da sai da aka fara muka gano ba ta da lafiya. Sannan na samar da jarumar da nake ganin ta yi daidai da labarin kuma za ta taimaka wajen fassara labarin yadda ya kamata ita ma ta bamu matsala.

Amma dai a yanzu mun fahimci mun samu matsaloli da kura-kurai wanda wasu ma daga wajena aka samu, duk da cewa labarin an ba shi cikakken hakkin sa, don babu wani da muka ɗakko da bai cancanta ba. Don haka a yanzu mun shata layi da yardar Allah ba za mu ƙara yin Kitso da Kwarkwata ba har zuwa ƙarshen aikin da kuma nuna shi a duniya.”

By ukarofi