
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya taya tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Super Eagles murnar samun kyautar ‘bronze medal’ sakamakon nasarar da ta yi a wasan neman matsayi na uku na gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025.
Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa wanke kansu da suka yi daga rashin nasara a wasan dab da na ƙarshe a hannun Moroko a ranar Larabar da ta gabata.
‘Yan wasan na Super Eagles sun nuna fin ƙarfi ga Masar da ta lashe gasar har sau bakwai, a zango bugun fenariti inda suka doke misrawan da ci 4 da 2.
A wani rubutu, Tinubu ya ce ‘yan wasan, bisa nasarar da suka samu, sun nuna bajinta da ƙoƙari, lamarin da ke da alaƙa da jajircewar Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana farin cikinsa ga tawagar inda ya ce: “za mu yi alfahari da su yayin da suke karɓar kyautar bronze medal mai wahalar samu a ranar Lahadi a Rabat, Moroko.”
A ƙarshe, ya kuma yi godiya a gare su da jagororinsu ganin yadda suka sanya Nijeriya da al’ummarta alfahari da su.
