Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Patrice Emery Lumumba na daga cikin fitattun jaruman Afirka da suka yi gwagwarmaya wajen kwato ’yanci daga Turawan mulkin mallaka. Sunansa ya shiga tarihi a matsayin Firaminista na farko na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan samun ’yanci daga Belgium a shekarar 1960. Lumumba ya shahara wajen tsayuwa tsayin daka, kishin ƙasa da kuma adawa da danniya da cin zarafin Afirka.
An haifi Patrice Lumumba a ranar 2 ga Yuli, 1925, a ƙauyen Onalua, cikin yankin Katanga na wancan lokaci a Belgian Congo (wanda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo). Ya fito ne daga ƙabilar Tetela. Tun yana ƙarami, ya nuna hazaƙa da son ilimi. Duk da cewa iyalinsa ba su da arziki, ya samu damar zuwa makaranta inda ya koyi karatu da rubutu cikin harshen Faransanci, abin da ya ba shi damar samun aiki a hukumomin gwamnati daga baya.
Lumumba ya fara aikinsa ne a matsayin ma’aikacin gidan waya, inda ya yi fice saboda kwazonsa da iya mu’amala. A wannan lokaci, ya fara karanta littattafan siyasa da na ‘yanci, musamman na shugabannin Afirka da na Turai masu adawa da mulkin mallaka. Wannan ne ya buɗe masa ido kan zaluncin da turawan Belgium ke yi wa al’ummar Congo.
A shekarun 1950, Lumumba ya shiga harkar siyasa sosai. Ya kafa jam’iyyar Mouvement National Congolais (MNC) a shekarar 1958, wacce manufarta ita ce haɗa kan ‘yan Congo ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba, domin su kwato ’yancinsu. Jam’iyyar ta samu karɓuwa sosai saboda Lumumba ya yi amfani da harshen gaskiya, yana sukar tsarin mulkin mallaka kai tsaye.
A taron ‘yan siyasa na Afirka da aka yi a Accra, Ghana, a shekarar 1958, Lumumba ya samu ƙarin kwarin gwiwa bayan haɗuwa da shugabannin ’yanci irin su Kwame Nkrumah. Bayan dawowarsa Congo, ya ƙara tsananta fafutukar neman ’yanci, lamarin da ya sa gwamnatin Belgium ta kama shi tare da tsare shi a wasu lokuta.
Duk da matsin lamba, gwagwarmayar ‘yan Congo ta yi ƙarfi. A ƙarshe, Belgium ta amince da ba Congo ’yanci a ranar 30 ga Yuni, 1960. A zaɓen da aka gudanar kafin ’yancin, jam’iyyar Lumumba ta samu nasara, inda aka naɗa shi Firaminista na ƙasar.
A ranar bikin samun ’yanci, Lumumba ya yi jawabi mai tarihi wanda ya girgiza duniya. Yayin da Sarkin Belgium ya yi jawabi yana yabon “kyakkyawan mulki” na turawa, Lumumba ya miƙe tsaye ya bayyana gaskiya, yana tuna wa duniya irin wulaƙanci, azaba da danniya da al’ummar Congo suka sha a lokacin mulkin mallaka. Jawabin ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya, amma ya ƙara masa karɓuwa a idon ’yan ƙasaraa.
Da zarar ya hau mulki, Lumumba ya fuskanci manyan ƙalubale. Rundunar soji ta yi bore, yankin Katanga ya ayyana ɓallewa, yayin da ƙasashen waje, musamman Belgium da Amurka, suka fara tsoma baki saboda tsoron Lumumba zai kusanci Tarayyar Soviet. Lumumba ya nemi taimako daga Majalisar ɗinkin Duniya (UN) don daƙile rikicin, amma ya ji an bar shi a gefe.
Saboda matsin lamba, Lumumba ya nemi taimakon Soviet, abin da ya ƙara tsananta tsoron ƙasashen Yamma. A wannan lokaci, shugaban ƙasa Joseph Kasa-Vubu ya tuɓe Lumumba daga muƙaminsa, shi kuma Lumumba ya ce ba ya amincewa. Rikici ya ɓarke a siyasar ƙasar.
A watan Satumba 1960, sojan da ake kira Joseph Mobutu (wanda daga baya ya zama Mobutu Sese Seko) ya yi juyin mulki da goyon bayan ƙasashen waje. An kama Lumumba, aka tsare shi, sannan daga baya aka tura shi yankin Katanga, inda abokan gabansa ke mulki.
A ranar 17 ga Janairu, 1961, aka kashe Patrice Lumumba tare da wasu abokan aikinsa biyu. An harbe shi ne a ɓoye, sannan aka ɓoye gawarsa domin kada ta zama abin tunawa. Daga baya aka gano cewa jami’an Belgium sun taka rawa a kisan, tare da goyon bayan wasu ƙasashen Yamma.
Mutuwar Lumumba ta girgiza Afirka da duniya baki ɗaya. Ya zama alamar kishin ƙasa da gwagwarmayar ’yanci. Shugabanni da dama na Afirka sun bayyana baƙin ciki, inda suka ɗauke shi a matsayin gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa domin al’umma.
Bayan mutuwarsa, sunansa ya zama abin koyi. An sanya sunansa a tituna, makarantu da filayen taro a ƙasashe da dama. A Congo, ana kallonsa a matsayin uban ƙasa da gwarzon juyin juya hali. Har yau, ana tunawa da shi a matsayin mutum mai tsayuwa tsayin daka da rashin tsoro wajen faɗar gaskiya.
A shekarun baya, gwamnatin Belgium ta amince da cewa tana da hannu a kisan Lumumba, inda ta nemi afuwa a hukumance. Wannan ya nuna irin zaluncin siyasar duniya da aka yi masa saboda tsayuwarsa kan gaskiya da ’yancin kai.
Patrice Lumumba ya bar tarihi mai girma a nahiyar Afirka. Kodayake rayuwarsa ta kasance gajeriya, tasirinsa ya zarce shekaru da dama. Ya koyar da duniya cewa ’yanci ba kyauta ba ne, sai an sadaukar. Ya kuma nuna cewa shugabanci na gaskiya yana buƙatar jajircewa, koda kuwa hakan zai kai ga rasa rai.
A yau, Lumumba ya zama alamar kishin ƙasa, adalci da mutunci. Tarihinsa na ci gaba da ba matasan Afirka kwarin gwiwa wajen tsayawa kan gaskiya da kare martabar ƙasashensu. Duk da irin ƙalubalen da Afirka ke fuskanta, sunan Patrice Lumumba na ci gaba da haskaka a matsayin fitila ga masu neman ’yanci da adalci.
